Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga mutanen Najeriya musamman ƴan Arewa su zaɓi ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a zaɓen shugaban kasa mai zuwa.
A wurin gangamin jam’iyyar APC wanda Buhari da kansa ya halarta tare da gaggan ƴan jam’iyyar APC a jihar Nassarawa, shugaba Buhari ya bayyana cewa Tinubu ne ɗan takarar sa kuma yana kira ga magoya bayan APC duka su zaɓe shi a zaɓe mai zuwa.
” Ku zaɓi Bola Tinubu ya shugabanci wannan kasa. Ɗan Najeriya ne na asali. Sama da shekara 20 muna gwagwarmayar siyasa tare da shi.
” Dukkan ku da ke nan idan kuka koma gidajenku ku gaya wa ƴan uwanku a ko ina suka su zaɓi Bola Tinubu shugaban kasa. Shine zaɓin mu duka.
Tinubu zai fafata da Atiku Abubakar Na PDP, Peter Obi na Labour Party, Rabiu Kwankwaso na NNPP a zaben shugaban kasa da za a yi a wannan wata.
”
Discussion about this post