Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana tare da dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar APC Bola Tinubu.
Buhari ya kara jaddada goyan bayan sa ga Tinubu da abokin takaransa Kashin Shettima sannan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su zabi ‘yan takaran jam’iyyar APC duka ranar 25 ga Fabrairu 2023.
Ya ce jita-jitan da ake ta yadawa wai baya goyan bayan Tinubu duk karya ne sannan ya kara da cewa zai ci gaba da kokarin ganin Tinubu ya yi nasara domin ganin APC ta ci gaba da mulki har bayan shekarar 2023.
Buhari wanda ministan sadarwa da tattalin arzikin Isa Pantami ya wakilce shi ya ce yana goyan bayan duk ‘yan takaran da jami’yyar APC ta gabatar.
“Ina goyan bayan duk ‘yan takarar da jami’yya ta ta gabatar sannan kuma ina tare da dan takaran Shugaban kasa na jami’yyar dari bisa dari.
“Don haka duk wanda ya zo ya fada muku akasin haka karya yake yi.
Ya lisafo aiyukka da dama da gwamnatin tarayya ta aiwatar a jihar Gombe da suka hada da aikin hako mai wanda ya ce an gano shekaru 40 da suka gabata amma ba a gudanar da bincike ba sai yanzu da yake shugaban kasa.
Buhari ya ce gwamnati sa ta aiwatar da aiyukka da dama na inganta kasa sannan ya kara da cewa Tinubu zai taimaka wajen tabbatar da nasarorin da aka samu daga farkon shigowar gwamnatin sa zuwa yanzu.
Discussion about this post