Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Ya kai Dan uwa mai girma! Lallai idan kana so kaga wauta, tanbada da lalata, to ka bari sai Dan arewa marar kishin al’ummarsa ya zama Gwamna! Irin wannan mutum, zai dauki sarakunansa ba kowa ba, malaman addininsa ba kowa ba, ‘yan kasuwarsa ba kowa ba, talakawansa ba kowa ba, kai duk wani Dan arewa mai kishi a wurinsa banza ne, shirme ne, wanda bai kai kimar a girmama ra’ayinsa ba, ko a mutunta shi.
Jama’ah, abun mamaki, wani naga ya fito yana cin mutuncin ‘yan uwansa ‘yan arewa, kawai don ya samu kansa a gadon mulki, wanda wannan mulkin da yake kai, nan da wasu ‘yan kwanaki ya zama tarihi, ya zama abun tausayi, domin za’a wayi gari ba shine akan wannan kujere ba, wani ne.
Kuma shi wannan mutum, ya dauka cewa wai shekaru sune dattako, bai san cewa halin mutum da mutuncinsa da girmama na gaba da kyawawan halaye da dabi’u nagari, da tausayi, da jinkai, da kishi, da tausayin talakawa, da marasa karfi, da marasa galihu, sune ke sa a kira mutum dattijo, ba shekarun sa ba! Domin irin wadannan halaye ne magabatanmu, Allah ya jikansu, irin su Sardaunan Sokoto da su Tabawa Balewa da su Aminu Kano suka nuna, sai al’ummah ta kira su dattawa, ba shekarun su ba!
Kuma shi wannan gwamnan fa, mai cin mutuncin manya, wai da yake cewa sune dattawan arewa, har yana cewa shi shekarunsa sittin da uku, kasancewar ya dauka cewa shekaru sune dattako, kwanan nan fa aka nuna shi yana tika rawa, yana cashewa, yana rawar disko, yana lankwasa jiki, yana karairaya a fili cikin taron jama’ah, babu kunya babu tsoron Allah, amma wai a haka shi dattijo ne!
Wannan fa shine kadan daga cikin halayen wadannan mutane masu kiran kan su sune dattijai, wai!
Yanzu domin Allah, mu yiwa kan mu adalci, mu tambayi kan mu, shin ana dattijo a haka? Amsa wallahi ita ce, a’a.
Kai wani gwamnan ma kallon dattawan jiharsa yayi, bayin Allah, mutanen kirki, masu daraja da mutunci, masu nufin sa da kuma jihar su da alkhairi, iyayen wasu, kakannin wasu, wadanda kowa yasan irin gudummawar da suka bayar wurin ci gaban wannan kasa da kuma al’ummarsu, ya kira su da DATTAWAN WUKARI, yaci mutuncin su, ya fada masu maganganun banza. Menene laifin wadannan mutane? Kawai laifin su shine, sun ce a gyara, domin jihar su taci gaba, kowa ya amfana, amma don rashin kunya da rashin mutunci, ya kira su da dattawan wukari, kawai don ya samu dama, ya zama gwamnan jihar!
Ai su yarbawan da yake magana, ba zasu taba cin mutuncin dan uwansu Bola Tinubu irin haka ba, ko menene kuwa yayi masu, saboda me, saboda su duk matsayin da suka kai basa raina mutanensu da manyansu, kuma basa raina ra’ayin al’ummarsu, basa raina yankin su da mutanensu. Amma Dan arewa da ya zama Gwamna, to a lokacin shi yana ganin babu wanda ya isa, babu wanda ya isa ya gaya masa gaskiya, ko ya bashi shawara, ko ya tuntube shi ya nuna masa matsalolin yankinsa da halin da al’ummarsa suke ciki.
Duk wani mutum mai mutunci da yake kokarin jawo hankalinsa domin ya taimaki al’ummarsa, ko ya tallafa masu akan abun da zai amfane su, to ba zai saurare shi ba. Shi yasa, har kullun, zasu yi mulkin nasu na shekaru takwas, amma daga karshe su kare mulkin, amma arewar tana nan yadda take, babu wani ci gaba. Kai bama wannan ba, har ma zaka ce gara da kafin su hau mulkin, da halin da muke ciki a yanzu.
A Inda zaka fahimci hakan shine, don Allah, don Allah, don Allah, daga lokacin da aka dawo mulkin dimokradiyyah, wato 1999 zuwa yau, shin yankin arewa gaba yaci ko baya? Amsar ita ce, ko dan ubayyu yasan da cewa baya muka ci wallahi! Ba zaka fahimci haka ba sai ka san irin hasarorin da muka tabka sanadiyyar rashin tsaro, tun daga rikicin Boko Haram, rikicin kabilanci da na addini, rikicin fulani da makiyaya, rikicin barayin shanu da barayin mutane domin karbar kudin fansa; wanda wadannan rikice-rikice sun mayar damu baya sosai ba kadan ba, ta fuskar tattalin arziki da dukkanin sassa na rayuwar mu! Kuma wallahi duk wadannan rikice-rikice sun samu ne sanadiyyar rashin iya shugabanci da irin wannan dagawa, girman kai, da raina mutane na Dan arewa idan ya samu wani matsayi.
Yaku ‘yan uwana ‘yan arewa, ku sani, wallahi a halin yanzu, ba ku da makiya, masu kokarin ganin bayan ku, irin wasu daga cikin Gwamnoninku. Sune sanadiyya, kuma sune ummul haba’isun shiga cikin halin da kuke ciki na kunci da wahala a yau. Kuma gashi yanzu, sun taru, sun yi gungu, domin su yaki ra’ayin ku, su tursasa maku goyon bayan wadanda baku so su mulke ku.
Duk dai kun ga irin abunda suka yi wurin zaben fitar da gwani (wato primary election) na jam’iyyar su. Sun sayar da ra’ayin al’ummarsu saboda abun duniya.
To ku sani, a halin yanzu, abun nan da suka yi a wancan zaben fitar da gwani, shi suke so su maimaita irin sa, na sayar maku da ‘yancin ku da ra’ayin ku, da kuma mutuncinku, wato suna nufin dole ku amince da wanda suke son su kawo maku, kawai ba domin maslahar ku ba, a’a, sai dai domin cimma wasu maslahohi nasu na kashin kansu!
To wallahi, yaku ‘yan uwana ‘yan arewa, ya zama dole, tilas, kuma wajibi, mu fito fili karara, mu nuna masu bamu yarda ba! Yanzu ne lokacin da ya kamata mu fito mu yake su wallahi.
Daga karshe, mu dai fatan mu, da addu’ar mu, da rokon Allah mu shine, Allah ya bamu shugabanni na kwarai, nagari, wadanda zasu zama alkhairi ga Musulunci, gare mu, ga Nigeria, da ‘yan Nigeria, ga arewa, da ‘yan arewa da kuma al’ummah baki daya, amin.
Ku sani, ko tikitin Muslim-Muslim, ko tikitin Muslim-Christian, duk daya ne. Duk wanda mutum yayi ra’ayi zai zaba daga cikinsu yayi daidai, bai sabawa Allah ba, bai yi zunubi ba, bai yiwa kowa laifi ba. Domin dukkaninsu wallahi babu wanda zai yi hukunci da dokokin Allah da Manzonsa (SAW). Dukkanin su zasu yi hukunci ne da tsarin mulkin Najeriya (wato constitution).
Kuma kar mu saurari masu kokarin yin amfani da addini ko kabilanci domin su kawo muna tashin hankali da rikici. Irin su Babachir, da su Dogara, da kuma wasu Malaman addini, masu kokarin Musuluntar da Tikitin Muslim-Muslim, kuma su kafirtar da Tikitin Muslim-Christian, wadannan duk domin kan su suke yi, ra’ayinsu suke yi, ba domin maslahar al’ummar su ba ne!
Ina mai jan hankulan ku, tare da fada maku gaskiya tsakanina da Allah, cewa kar ku sake ku saurari wadannan mutane, wato Babachir da Dogara da kuma wadancan Malaman addinin, masu kokarin yaudararmu da cewa wai tikitin Muslim-Muslim addini ne, domin dukkanin su idan arewar ta rikice, aka fara kashe-kashe da kone-kone, wallahi ba zaka taba ganin ‘ya ‘yansu a cikin ko wace irin hayaniya ba. ‘Ya ‘yan talakawa ne kadai za’a yi ta kashewa a banza!
Sam bai kamata addini ya zama abun wasa ba. Bai kamata mu kawo maganar addini da kabilanci, muna kokarin haddasa gaba da kiyayya da rikice-rikice da tashe-tashen hankula da zubar da jinin bayin Allah a cikin al’ummah ba!
Haba don Allah! Addini ya zama bai da wata daraja a wurin ku sai an zo maganar siyasa, sai kuyi kokarin amfani da shi domin cimma wasu manufofinku?
Wallahi muji tsoron Allah. Kar mu yarda mu bayar da gudummawa wurin kara rugujewar arewa, da kara tarwatsa ta!
Magabatan mu irin su Sardaunan Sokoto, Tabawa Balewa, Ribadu, Isa Kaita, Aliyu Makaman Biddah, Dan Masanin Kano, Aminu Kano, Sa’adu Zungur, Abdur-Rahman Okene, da ire-irensu, ba haka suka yi ba wallahi.
Kuma mu sani, mu a arewa yanzu babu abunda ya rage muna sai mulkin nan, idan kuma muka yi sakaci, muka yarda ya sulale, to ya rage namu…!
Allah ya jikan magabatanmu, wasu daga cikin su suna cewa:
“MU HADU MUYI AIKI TARE, AMMA KOWA YASAN GIDAN UBANSA!”
Wannan magana tasu kuwa haka ta ke. Domin duk wani Dan arewa da yake zaune a wani yanki wanda ba nasa ba, yasan irin abinda yake gani a fili karara!
Kuma duk wani Dan Najeriya, da duk wani Dan arewa, yasan abun da yake ji a jikinsa, kuma mun san irin wuya da wahalar da muka sha karkashin wadannan mutanen. Don haka, ya zama tilas, dole, kuma wajibi, muyi amfani da damar da Allah ya bamu mu dakatar da su ta kowa ne hali!
Wahalhalun da muka sha sun isa haka nan. Dole ne mu canza wadannan mutanen da wasu, da kuma niyyah kyakkyawa, sai Allah ya taimake mu!
Idan kuma munki ji, to lallai ba zamu ki gani ba. Domin Malam bahaushe yace: JIKI MAGAYI!!!
Kuma Dan uwana ka sani, wannan ra’ayi nane, kuma fahimta tace, kai ma ban hana ka kayi naka ra’ayin ko taka fahimtar ba!
Allah yasa mu dace da shugabanni nagari, amin.
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau – 08038289761. Juma’ah, 03/02/2023.
Discussion about this post