Hukumar ICPC ta bada sanarwar damƙe wata matar da ake zargi ta na sayar da sabbin takardun nairori ga mabuƙata wurjanjan, ta intanet.
Matar wadda ake zargi mai suna Oluwadarasimi Emma, ta yi amfani da shafin ta na Twitter ne mai suna Simisola of Lala, yanzu haka an tsare ta bisa zargin ta na amfani da shafin ta na sada zumunta ta na sayar da sabbin kuɗaɗe, kamar yadda Kakakin ICPC, Azuka Ogugwa ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
ICPC ta ce an yi amfani da bayanan leƙen asiri aka bi diddigin wadda ake zargin, har aka cim mata, aka damƙe ta.
Matar ta na sana’ar sayar da kayan gyaran jiki na mata, ta yi amfani da matsalar ƙarancin sabbin kuɗaɗe, ta buɗe harkar sayar da sabbin kuɗi.
ICPC ta ce akwai yiwuwar matar ta haɗa baki ne da wasu taƙadaran ma’aikatan banki wajen gudanar da wannan haramtacciyar sana’ar da aka kama ta na aikatawa.
Matar baya ga sayar da kayan gyaran jiki na mata, kuma ta na sayar da fetur, ya na harkar ejan ga masu fita ƙasashen waje ta hanyar samar masu biza da sauran harkokin hada-hada.
A yanzu ta na tsare a hannun jami’an ICPC, kuma za a gurfanar da ita da zaran an kammala bincike.