Hukumar EFCC ta maida kakkausan raddi kan gungun wasu mutane da su ka yi zanga-zangar neman a cire Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa, inda hukumar ta ce “sojojin haya ne aka ɗauko aka biya su domin kawai su shiga zugar zanga-zanga.
EFCC ta ce wasu ‘yan kwatagwangwamar da ke neman kuɓuce wa binciken da ake yi masu ne su ka shirya zanga-zangar, amma kuma ba za su yi nasarar kuɓuta ba.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka, a lokacin da ya je wa manema labarai jawabi, a madadin Bawa, Shugaban hukumar.
Uwujaren ya bayyana cewa “haya aka ɗauko gungun matasan domin su yi zanga-zangar a biya su.
Ya ce EFCC ba za ta razana ba, kuma ko kaɗan ba za su karkatar da hukumar domin ta daina binciken su ba.
EFCC ta ce rahotannin da ta samu sun gamsar da hukumar cewa, “wasu manyan ƙadangarun da EFCC ke kan bincike ne su ka shirya zanga-zangar ta bayan fage kuma su ka biya su.”
Ya ce masu zanga-zangar sun yi hardar kalaman tozartawa ga Shugaban EFCC, waɗanda za su ci gaba da watsawa a faɗin ƙasar nan, har sai an cire masu Bawa.
Uwujaren ya ce ƙungiyar da ta shirya zanga-zangar ba ta da wata alaƙa da kishin ƙasa ko kishin al’umma. Ya ce muradin ta kawai ya haɗa rikici ta yadda za su haɗa jama’a su yi wa Bawa bore.
An dai samu rahotonnin zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna Coalition of Anti-Corruption Organisations, waɗanda su ka yi kiran Shugaban EFCC, Bawa ya sauka.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zanga ɗin mai suna Ayodeji Ologun, ya yi kira ga Shugaba Buhari ya yi wa EFCC garambawul, domin ya maida ta cikin martabar da aka san hukumar na ciki a shekarun baya.
Masu zanga-zangar sun hasala ne daga hukuncin da V
Babbar Kotun Jihar Kogi ta yanke, inda ta nemi Sufeto Janar ya damƙe mata Bawa, saboda ya ƙi bin umarnin kotu.
Wani ɗan uwan Gwamna Yahaya Bello na Kogi ne, mai suna Ali Bello ya shigar da ƙarar, inda ya ƙalubalanci kamun da Bawa ya yi masa a matsayin haramtacce.
EFCC ta damƙe ɗan’uwan na Yahaya Bello bisa wani zargi na biyu, na karkatar da Naira biliyan uku.