Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama Michael Ogundele mai shekara 30 da ake zargin bindige saurayin budurwarsa Tobi Olabisi.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka ranar a garin Abeokita, babban birnin jihar Ogun.
Oyeyemi ya ce ‘yan sanda sun kama Ogundele ranar Juma’a a gidansu kuma a inda ya harbe saurayin kanwarsa Olabisi dake Idi-Iroko a karamar hukumar Ipokia.
Ya ce dama Ogundele baya son yadda Olabisi ke bibiyar kanwarsa da a duk lokacin da suka hadu yake jan kunnen sa cewa ya rabu da ita amma ya ki.
“Wata rana sai wasu ƴan unguwan suka faɗi wa Ogundele cewa ga Olabisi can yana kwance a gado tare da kanwarsa a cikin gidan su.
“Tashin Ogundele ke da wuya sai ya dauki bindiga ya shiga dakin kanwar sa sai dai kafin ya karisa dakin Olabisi ya fice ta taga. Sai dai kafin ya tsallaka Olabisi ya ɗirka masa bindiga.
Bayan hakan ya faru sai dagacen kauyen Alpha Akeem ya je ofishin ‘yan sandan dake Idi Iroko tare da Olabisi domin kai kara.
Oyeyemi ya ce da ya shiga hannun jami’an tsaro Ogundele ya bayyana yadda ya rika jan kunnen Olabisi da ya daina bibiyar kanwar sa amma ya ki.
Kakakin rundunar ya ce Olabisi na babban asibitin Idi Iroko likitoci na duba shi sai dai bai fadi inda ya ji rauni ba.