Yayin da ya rage saura kwanaki 25 a yi zaɓen shugaban ƙasa na 2023, har yau Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya kasa bayyana sunan ɗan takarar shugaban ƙasa wanda zai mara wa baya har ya taya shi kamfen, kamar yadda ya yi alƙawarin bayyanawa a cikin watan Janairu.
Idan za a tuna, tun a cikin watan Nuwamba, 2022 Wike ya ce a cikin Janairu 2023 ne zai bayyana sunan ɗan takarar shugaban ƙasa wanda Ai yi wa kamfen ɗin goyon bayan lashe zaɓen shugaba ƙasa.
Cikin watan Disamba ma Wike ya maimaita wannan alƙawari da ya yi.
Sai dai kuma ganin cewa a yau ranar Laraba, watan Janairu ya ƙare har an shiga Fabrairu, amma Wike bai bayyana ba.
Kakakin Wike ya shaida cewa har yanzu Gwamnan bai kai ga bayyanawa ba tukuna.
Cikin watan Disamba dai Wike ya yi alwashin cewa zai bayyana wanda zai goyi baya a zaɓen shugaban ƙasa a cikin watan Janairu.
To ga shi Janairu ya wuce amma Wike bai bayyana ɗin ba.
Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya bayyana cewa a cikin watan Janairu 2023 ne zai bayyana sunan ɗan takarar shugabancin ƙasa wanda zai ce al’ummar jihar Ribas su zaɓa.
Wike ya yi wannan furucin a ranar Alhamis, lokacin da ya ke buɗe wata gadar sama wadda ya gina a Fatakwal.
“Da masu jira su ji daga baki na da masu zagi na, duk su jira ai watan Janairu ya zo. A cikin sa zan bayyana sunan ɗan takarar shugaban ƙasa wanda zan ce ‘yan Jihar Ribas su zaɓa.
“Kuma ba zaɓen sa kaɗai zan sa a yi ba, har ma kamfen zan taya shi ana karakaina da ni daga wannan jiha zuwa wannan. Kuma babu abin da zai faru.”
Wike shi da wasu gwamnoni biyar dai har yau ba su amince da takarar Atiku Abubakar a PDP ba, su na masu jayayyar cewa lokaci ne da ɗan kudu zai yi mulki, ba ɗan Arewa ba.
Sai dai kuma daga baya sun nemi Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu shugabancin jam’iyya, sannan su amince da takarar Atiku.
Baya ga Wike, akwai Samuel Ortom na Benuwai, Ikpeazu, akwai kuma Seye Makinde na Oyo.
Har yau ba su taɓa taka inda Atiku ke kamfen na takara ba, kuma ba a ga alamar sasantawa a fuskokin su ba.
Yayin da su ka ce ba su yarda su mara wa Atiku baya ba saboda daga Arewa ya fito, akwai masu takarar shugabancin ƙasa daga ɓangaren Kudu, wato Bola Tinubu na APC da kuma Peter Obi na LP. Kuma dukkanin su sun yi zawarcin Wike a baya.
Idan ba a manta ba, cikin Nuwamba ne Wike ya ce zai bai wa Peter Obi da rundunar sa kyakkyawan masauki idan sun je kamfen a Ribas.
Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya bayyana cewa zai yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Nyesom Wike kyakkwar tarba da yi masu hidimar da ta kamata idan su ka je jihar Ribas kamfen.
Wike, ɗaya daga cikin gwamnoni biyar ɗin da su ka yi wa PDP tawaye, ya bayyana haka a lokacin da ya gayyaci Obi wurin buɗe wata shantaleliyar gadar sama da ya gina a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Wike wanda ya gina gada ta bakwai kenan a jihar sa, ya jinjina wa Obi dangane da takarar shugaban ƙasa da ya ke yi a ƙarƙashin jam’iyyar LP, ya na mai cewa Obi ya cancanci ya mulki Najeriya.
Dukkan su biyu ɗin dai sun nemi takarar shugaban ƙasa a PDP, inda kafin zaɓen fidda gwani sai Obi ya fice ya koma LP, kuma aka ba shi takara a can, shi kuma Wike bayan ya faɗi zaɓe ya haɗa kai da wasu gwamnonin PDP huɗu su ka bijire, su ka ƙi goyon bayan takarar Atiku Abubakar da shugabancin Iyorchia Ayu.
Gwamna Wike ya bada sanarwar bai wa Obi da rundunar kamfen ɗin sa haɗin kai ya yi taron sa lafiya a wuraren da za a yi taron, bayan ya kafa ƙarfa-ƙarfar dokar hana sauran jam”iyyu amfani da wuraren taruka a jihar sa.
A na sa ɓangaren, Obi ya yi murna da zuwa Ribas, inda ya ce dama shi Fatakwal gida ce, domin a Fatakwal ya yi makaranta, kuma har yanzu bai yi watsi da abokan karatun sa da ke zaune a jihar ba.
Discussion about this post