Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne ya yi nasara a zaɓen shugaban kasa da aka bayyana a jihar Kaduna.
Bisa ga sakamakon zaɓen da baturen zaɓe ya bayyana a garin Kaduna ranar Talata Atiku na jam’iyyar PDP ya samu Kuri’u 554,360 inda Bola Tinubu na APC ya samu Kuri’u 399,293.
Bisa ga sakamakon kananan hukumomi da aka bayyana, PDP ta lashe kananan hukumomi 13, LP ta samu kananan hukumomi 7, sai kuma jam’iyya mai mulki ta yi nasara a kananan hukumomi 3 ne kacal.
Jam’iyyar Labour ta samu Kuri’u 294,494 sai jam’iyyar NNPP, jam’iyyar Kwankwaso ta samu Kuri’u 92,972.
APC ta rasa sanatoci 2 da take da su a majalisar dattawa, inda PDP ta kwace su. Sai kuma ƴan majalisun tarayya da ta tashi da kujeru uku kacal cikin 13.
Discussion about this post