Tsohon Ministan Sadarwa a zangon Shugabancin Buhari daga 2015 zuwa 2019, Adebayo Shittu, ya ce azaba da ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya ke sha a yanzu sakamakon ƙarancin fetur da sauya launin kuɗi, duk alamomi da hujjoji ne masu nuna gazawar shugabanci.
Shittu da ya yi wannan bayani a lokacin da ake ganawa da shi a gidan talabijin NA AIT, a ranar Alhamis.
‘Yan Najeriya na ci gaba da zaman wahalar ƙarancin fetur da kuma tsadar sa, inda wasu garuruwa ake sayen duk lita ɗaya naira 400.
Haka kuma sauya launin kuɗin da CBN ya yi ya haifar da tsugunnewar harkokin rayuwa da na tattalin arziki a faɗin ƙasar.
Rashin Iya Shugabanci Ne – Adebayo Shittu:
Shittu ya ce wannan wahala da ake fama da ita, abin takaici ce, kuma laifin waɗanda su ka ƙirƙiro ta ce.
“Abin kunya ne kuma abin takaici ce abin da ke faruwa yanzu a Najeriya. Rashin iya shugabanci ne. Kuma laifin waɗanda aka ɗora wa tafiyar da ɓangarorin ne.”
Shittu ya ce Buhari salihin mutum ne, kuma shiru-shiru wanda bai cika magana sosai ba. Dalili nekan wasu tsirarun ‘yan ba-ni-na-iya da ke kewaye da shi ke yin abin da su ka ga dama.
“Sauya launin kuɗi abu ne mai fa’ida kuma abin da ya dace. To amma ba za ka yi nasara ko da abin ya dace ba, sai idan an aiwatar da tsarin a lokacin da ya dace.
“Tilas mu tashi mu ragargaji gwamnati saboda ta yi canjin kuɗi a lokacin da bai dace a yi canjin ba.
“Ni ina ganin ba a bai wa Shugaba Buhari cikakken bayanin yadda batun sauya launin kuɗin ya ke ba. Ba a baje masa komai a faifai ba, an ba shi lamarin ne kawai a lulluɓe.” Inji Shittu.
Shittu ya ce idan Buhari bai shawo kan wannan matsala a cikin sati biyu ba, to idan ya sauka zai shiga matsala sosai.
Daga nan ya yi kiran cewa a daina ɗora wa ɗan takarar APC, wato Bola Tinubu laifin gazawar wannan gwamnati.
Discussion about this post