Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari cewa ya soke tsarin sabbin kuɗaɗen da ya shigo da shi, domin lamarin ya haifar da matsananciyar wahala ga talakawa.
A ranar Asabar ce Akeredolu ya yi wannan bayani a Akure, babban birnin jihar, a cikin wata sanarwar da ya fitar.
“Tsarin sauya launin kuɗin da CBN ya ƙaƙaba ya kusa da hargitsa zaɓen 2023 da kuma dimokraɗiyyar ma ɗungurugum.”
Akeredolu ya ce kwan-gaba-kwan-bayan da aka riƙa yi cikin makon da ya gabata, raina umarnin Kotun Ƙoli da kuma tarzomar ƙone-ƙone bankuna babbar barazana ce ga dimokraɗiyya.
“Saboda haka ya kamata duk wani mai kishin ƙasa ya fito ya yi magana, domin a samu mafita, ba kawai a riƙa sa son rai ba.” Inji Akeredolu.
Ya roƙi Buhari ya nuna halin dattako, ya janye shirin, ganin yadda ƙasar ta dau zafi.
Akeredolu ya ce CBN ya Yi shisshigin ƙaƙaba tsarin a lokacin da bai dace ba.
Shi kuwa tsohon Kwamishinan INEC ya yi gargaɗin kada fa jama’a su ƙaurace wa fita zaɓe.
Bisa la’akari da mawuyacin halin da aka ƙaƙaba wa ‘yan Najeriya na ƙarancin fetur da ƙarancin sabbin kuɗaɗe, tsohon Kwamishinan INEC Lai Olurode ya yi gargaɗin cewa kada a a haddasa yanayin da jama’a za su ƙaurace wa fita su yi zaɓe.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Olurode ya ce hanya ɗaya da za a iya magance wannan masifa ita ce a fita a zaɓi shugaban da zai iya kawo ƙarshen lamarin.
“Idan mu ka yi la’akari za mu fahimci cewa shugabannin da ake azabtar da jama’a sun fi so su ga jama’a da yawa ba su fita sun yi zaɓe ba. To sai fa idan mu da ake zalunta mun fito dafifi mun yi zaɓe sannan za mu iya yin maganin su.”
“A ƙasar nan na fahimci ana so ne kawai jama’a su ƙaurace wa zaɓe. An ƙirƙiro wahala da tsadar fetur. An ƙirƙiro masifar ƙarancin sabbin kuɗi da jangwangwamar canjin kuɗin ita kan ta. Kuma duk manyan ƙasa ne masu neman madafun iko ke faɗa a tsakanin su, amma kuma mu abin ke wa illa.”
Daga nan ya ce mafita kawai ita ce mu yi tururuwa mu fita mu yi zaɓe a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023.
A ƙarshe ya ce fita ana zanga-zanga ba shi ne mafita ba. Mafita kawai ita ce a yi dafifi a fita a jefa ƙuri’a.
Discussion about this post