Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya soki sabbin sauye-sauye da shugaban kasa ya bijiro da su a dai dai jajibirin zaben 2023.
Saura akalla makonni uku da ‘yan kai a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya amma kuma abin mamaki shine yadda jam’iyya mai mulki ta ke neman ruftawa cikin rudanin da zai iya sa ta rasa kujerar shugaban kasa a zaben.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai a hira da yayi ta talbijin din channels ya zargi wasu gwaskaye a fadar shugaban kasa dake yi wa takarar Bola Tinubu bita da Kulli domin kawai basu so ya zama shugaban kasa.
El-Rufai ya ce : Babu alfanun da canjin kudi zai yi wa kasa a dan kankanin lokaci irin haka da zabe ya karato da dole sai an yi su. Sannan kuma matsalolin wahalar mai da ake fama da shi da gangar aka kirkiro shi domin a kawai mutane su yi wa jam’iyyar bore, su ki zabar ta a zabe mai zuwa.
” Nan ni da kai na tare da wasu gwamnoni muka je fadar shugaban kasa muka ba shi shawarwain yadda za a kawo karshen matsalar mai, kuma har kudirori muka aika majalisa akai amma shiru, sannan kuma wadanda ke da ikon tabbatar da abin ba a hukunta su ba.
” Maganar sauya launin kudi kuwa, babu wani alfanu da sauya kudi zai yi wa Najeria a wannan dan kankanin lokaci, kuma wai sai da aka tunkari zaben kasa sannan ace wai za a bijiro da irin wannan abu haka. Tsakani da Allah dole talaka ya fusata ya yi wa jam’iyyar Bore ba.
El-Rufai ya ce adaina ganin laifin Emefiele kan sauya launin kudin kasa, idan ba a manta ba shima shugaba Buhari na da tarihin sauya launin kudi ba tun yanzu ba don bankado masu harkalla.
Discussion about this post