Mahara sun kai wa zugar ‘yan kamfen ɗin ɗan takarar sanata Oforchukwu Egbo hari, mai wakiltar PDP a Enugu ta Arewa.
An buɗe masu wuta ne a ranar Laraba, daidai Eke-Out da ke yankin Amechi Awkunanaw cikin Ƙaramar Hukumar Enugu ta Kudu.
Farmakin ya faru daidai lokaci da kuma wurin da aka bindige ɗan takarar sanatan LP na Enugu ta Gabas.
Sai dai har yanzu ba a sani ba ko waɗanda su ka kashe ɗan takarar LP su ne su ka kai wa ɗan takarar PDP ɗin hari ba.
Yayin harin dai an bindige direban ɗan takarar. Amma dai wakilin mu ya tabbatar cewa Egbo ba ya cikin motar da aka bindige ɗaya daga cikin direbobin na sa.
An riƙa watsa bidiyon hoton gawar direban a wurin da aka bindige shi, a cikin motar da yake tuƙawa.
Bidiyon ya nuna yadda direban ya yi mummunar ƙonewa a cikin motar.
Wani ɗan Majalisar Tarayya ɗan PDP daga Jihar ya tabbatar da faruwar munmunan harin.
Haka kuma wannan jarida ta buga labarin cewa an bindige ɗan takarar sanatan jam’iyyar Peter Obi a Enugu.
Wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wa ba ne sun bindige ɗan takarar sanatan jam’iyyar LP na Enugu ta Gabas, a yankin Amechi Awkunanaw, cikin Ƙaramar Hukumar Enugu ta Gabas.
An bindige Oyibo Chukwu ne a ranar Laraba, tare da wasu magoya bayan sa biyar waɗanda ke cikin mota ɗaya tare da shi.
Kisan ya faru ne kwanaki uku kafin zaɓen sanatoci, wanda za a yi tare da na shugaban ƙasa a ranar Asabar, 25 ga Fabrairu, 2023.
Shugaban jam’iyyar LP na Jihar Enugu, Casmir Agbo ya tabbatar wa PREMIUM TIMES a ranar Alhamis ɗin nan labarin wannan mummunan kisan gilla.
“E, gaskiya ce an bindige shi. A yanzu haka mu na zaman taron ganawa kan batun na mutuwar ta shi.”
Agbo ya yi zargin cewa kisan ɗan takarar na da alaƙa da siyasa, ba ‘yan bindigar da ba a sani ba ne.
Wata majiya mai kusanci da ɗan takarar da aka bindige ɗin, ya tabbatar wa wannan jaridar cewa tabbas an kashe ɗan takarar.
Ya ce bayan sun kashe shi kuma sun ƙone gasar sa.
“Babbar matsalar ita ce da ba shi da jami’an tsaro masu kare lafiyar sa. Haka ya ke kamfen ko’ina ba jami’an tsaro masu gadi ko kare lafiyar sa.”
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Enugu, Daniel Ndukwe ya tabbatar da labarin kisan, amma kuma ya ce a saurare shi sai an jima zai yi cikakken bayani.
Ba wannan ne karo na farko da aka kai wa ‘yan LP hari a lokacin kamfen ba.
A ranar 4 Ga Satumba, ‘yan bindiga sun kai wa mambobin LP hari a lokacin da su ke taro a Karamar Hukumar Awgu.
Haka ma a cikin Disamba sun kai irin wannan hari a jihar Imo.
Sai dai kuma wasu mambobin LP na zargin cewa wasu jam’iyyu ne ke ɗaukar nauyin hare-haren saboda haushin karɓuwa da farin jinin da LP ta yi.