Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya fallasa zargin cewa akwai wasu ‘ƙadangarun bariki’ a cikin Fadar Shugaban Ƙasa, waɗanda ba su fatan Bola Tinubu ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa.
“Na yi imani da cewa a cikin Fadar Shugaban Ƙasa akwai wasu ƙadangarun bariki masu so mu faɗi zaɓen shugaban ƙasa, saboda kawai su ba su samu abin da su ke so ba. Saboda ɗan takarar su bai yi nasara a zaɓen fidda gwani ba.”
Nasir El-Rufai ya yi wannan iƙirarin a ranar Laraba, yayin da ya ke tattaunawa da gidan talabijin na Channels TV.
Ya ce waɗannan ƙadangarun bariki wani ɗan takara daban su ka so ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, ba Bola Tinubu ba a APC.
Ya ce waɗannan mutane a yanzu su na fakewa bayan Shugaba Muhammadu Buhari su na ƙaddamar da mummunar aniyar son ran su.
“Sai ƙoƙari da gaganiya da zagon ƙasa da yi mana taɗiya su ke yi domin su ga mun faɗi zaɓen 2023. Sun fake bayan Shugaban Ƙasa su na abin da shi Buhari ke ganin daidai su ke yi.” Inji El-Rufai.
El-Rufai ya ragargaji canjin launin kuɗi da ƙarin kuɗin fetur da kuma wahalar sa da ƙarancin sa.
“Shugaban Ƙasa na da ikon sauya launin kuɗi. To amma fa a daidai wannan lokacin, babu wani tasiri ko alfanu da canjin kuɗin zai haifar a siyasance ko kuma ga tattalin arzikin Najeriya.
“Shi ma batun janye tallafin fetur, wanda ke janyo wa Najeriya asarar tiriliyoyin da yawa, abu ne da dukkan mu ka amince cewa a cire shi. Domin har ma zama sai na na yi ni da Shugaban Ƙasa, na fayyace masa dalilin da ya sa tilas a cire tallafin fetur.
“Saboda ta yaya za ka yi kasafin manyan ayyukan gina titina na naira biliyan 200, sannan ka koma ka kashe naira tiriliyan 2 a wajen biyan kuɗin tallafin fetur?
“Wannan ne batun da na tattauna da Shugaban Ƙasa, tun cikin 2021, lokacin da ake hayaniyar matsalar kuɗin tallafin fetur.”
Idan za a tuna, Tinubu shi ma a makon da ya gabata ya yi zargin cewa an ƙirƙiro ƙarancin fetur da sauya launin kuɗi ne don kawai a kayar da shi zaɓen 2023.