Daya daga cikin yan takarar shugaban kasa da aka fafata da shi a zaben da aka kammala ya roki sauran yan takaran su maida takubban su su dauki dangana.
Adewole Adebayo wanda shine dan takarar shugaban kasa na SDP ya ce shima bai ji dadin abinda ya faru ba amma a nasa ganai abinda ke faruwa daidai ne abinda mutane ne suka zaba.
” Nima fa na yi takarar nan, amma kuma mautane ba su zabe ni ba, sakamakon da ake bayyanawa shine abinda jama’a suka zaba. Kamata yayi Obi da Atiku su dauki dangana su kira Tinubu su su taya shi murna kawai a wuce wurin amma hukumar zabe ta yi kokarin gaske a wannan zaben.
” Me ya sa mu ke so mu tado fitinar dababu ita. Nan muke ta sukar abinda Trump na Amurka lokacin da ya nemi tada zaune tsaye a lokacin zaben kasar, muna cewa bai yi daidai ba. Amma kuma daga karshe dolen sa ya mika mulki ya kara gaba. Haka a nan ma ba zai canja zani ba. Wadanda suka fadi su yi hakuri su maida takobin.
Saboda haka abinda ya fi dacewa shine in hakura, idan ana kammala komai kuma jam’iyyata ba su gamsu sai mu garzaya kotu.
A karshe ya yi kira yan takara su yi koyi ga irin abinda tsohon shugaban kasa yayi, a 2015, da ya kira Buhari da yayi nasara ya taya shi murna.