Ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika ya bayyana cewa ba zai taba goyon bayan dan takarar Shugaban kasa na jami’yyar LP Peter Obi ba saboda banbancin akida a siyasance da suke dashi.
Hadi Sirika ya rubuta a shafin sa ta Tiwita cewa banbancin ra’ayi da akida a siyasance dake tsakanin su.
Ya kara da cewa Bola Tinubu ne dan takarar sa wanda zai yi wa aiki yake kuma fatan zai yi nasara a zaben dake tafe.
“Akida ta da na Obi ba daya bane sannan ra’ayinsa da matsayarsa kan wasu batutuwa ya banbanta da nawa shi ya sa na na yin sa kwatakwata. Ni APC nake yi shi kuma LP. Asiwaju shine dan takara na.