Rundunar Amotekun dake jihar Osun ta kama Wani mutum mai shekara 47 da ake zargi ya yi sata a cocin Seraphim dake Ogo-Oluwa a Osogbo.
Kwamandan rundunar Bashir Adewinmbi ya ce mutumin ya shiga cocin da misalin karfe 4 na safiyar wannan rana lokacin da babu kowa a cocin.
Adewinmbi ya ce rundunar ta kama wannan barawon bayan karar da wani ya kawo ofishin yan sandan.
Ya ce suna samun wannan kara sai suka yi gaggawar zuwa cocin inda suka cafke barawon tare da kayan da ya sace.
Adewinmbi ya ce rundunar ta kama barawon da na’urar hada sauyi, na’urar microphones, ganguna da sauran su.
Ya ce sun damka barawon hannun rundunar ‘yan sandan jihar domin ci gaba da bincike.
Adewinmbi ya yi kira ga mutane da su ci gaba da hada hannu da jami’an tsaro ta hanyar tona asirin duk masu aikata laifuka cewa yin haka zai taimaka wajen rage yawan haka a jihar.