Babbar Kotun Tarayya da ke Wuse Zone 2, Abuja, ta umarci Babban Bankin Najeriya CBN cewa ya tabbatar bai ƙara ko kwana ɗaya daga ranar 10 Ga Fabrairu na wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗaɗen naira ba.
Mai Shari’a Eleojo Enenche ne ya bayar da wannan hukunci a ranar Litinin, a ƙarar da wasu jam”iyyun siyasa huɗu su ka kai CBN kotu.
Jam’iyyu huɗu da su ka ƙunshi AA, APP, APM da NRM sun shigar da ƙara cewa bankunan kasuwanci ne ke wa sabon tsarin canjin kuɗi ƙafar ungulu.
Sun kai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da wasu bankuna 25 ƙara kotu.
Kotu ta umarci Buhari, CBN, Gwamnan CBN da bankuna 25 kada su ƙara wa’adi daga ranar 10 Ga Fabrairu, har sai kotu ta kammala sauraren ƙorafin jam’iyyun huɗu tukunna.
Kotun kuma ta aika wa bankunan 25 sammacin su je su yi bayanin dalilin da ya sa ba za a gurfanar da su ba, saboda sun kawo zagon ƙasa, ta hanyar ɓoye sabbin kuɗaɗe, sun ƙi bai wa kwastomomi sabbin naira 200, naira 500 da naira 1,000.”
A ranar Litinin EFCC ta bayyana damƙe wani manajan banki, saboda ya danƙare maƙudan sabbin kuɗaɗe, ya ƙi bai wa kwastomomi.
Sai dai kuma EFCC ba ta ambaci sunan sa ko sunan bankin sa manajan ke aiki ba.
Wannan umarni na Babbar Kotun Tarayya ya zo ne bayan Gwamnonin APC uku sun garzaya Kotun Ƙoli, sun shigar da ƙara cewa wa’adin ranar 10 Ga Fabrairu da za a daina karɓar tsoffin kuɗaɗe ya yi kaɗan.
Gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara ne su ka garzaya kotun, su na buga misali da irin baƙar wahalar da ‘yan Najeriya ke sha, sakamakon ƙarancin sabbin kuɗaɗe.