Sau uku tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya na buga gasar daga kai sai mai tsaron gida, wato bugun fenaritin gasar shiga Fadar Shugaban Ƙasa, amma bai taɓa jefa ƙwallo a raga ba.
Zaɓen da INEC za ta gudanar a ranar 25 Ga Fabrairu, zai kasance wata dama ɗaya tilo da ta rage wa Atiku ya jefa ƙwallo ɗaya tilo, domin ya samu nasarar zama shugaban ƙasa.
A matsayin sa na babban ɗan adawa ga jam’iyya mai mulki, za a iya cewa duk wata matsalar da APC ke ciki, to alheri ce ga Atiku. Gagarimar matsalar faɗan cikin gida da APC ke fama da shi, ƙasa da kwanaki 21 kafin zaɓen 2023, za ta iya zama tagomashi ga Atiku Abubakar.
To sai dai tun da farko PDP ta yi sakacin kasa ɗinke ɓarakar da Peter Obi na LP ya fusata har ya kauce daga PDP, ya tsaya takarar shugaban ƙasa a LP.
Irin hakan ne ya fusata Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya fice, ya samu takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin NNPP.
Duk da cewa mutanen Kwankwaso da na Obi a yanzu ba su cikin PDP, kuma jama’a sun ragu a jam’iyyar kenan. Sai dai kuma matsalolin da ake gaganiya kan su har ake jin haushin APC, ya sa PDP ta ƙara cika da hasalallun da ke jin haushin ƙuncin rayuwar da ake fama da ita kamar canjin kuɗi da tsadar fetur su na ta maida goyon bayan su kan Atiku, Kwankwaso ko Peter Obi.
Komawar ‘yar taratsi Najatu Mohammed ɓangaren Atiku bayan ta yi wa Tinubu wulaƙanci duk duniya ta shaida, hakan ya ƙara zaburar da Atiku, har ji ya ke yi kamar ya fara jin ƙamshin kujerar mulkin da Buhari zai sauka a kai ranar 29 Ga Mayu, 2023.
Sai dai kuma wani sabon ruɗani ya kunno kai daga kudancin ƙasar nan a farkon wannan wata na zaɓen 2023. Dattijo Shugaban Kungiyar Dattawan Neja Delta, Edwin Clark ne ya ce Gwamna Ifeanyi Okowa mai wa Atiku Abubakar takarar mataimakin shugaban ƙasa, ya fito ya janye takarar sa, kuma ya nemi afuwa.
Edwin ya ce Okowa ya ci amanar ‘yan kudancin ƙasar nan. Sannan kuma ya ce Atiku ba zai ci zaɓen 2023 ba.
Wata matsala da Atiku ke fama da ita, ita ce yadda ƙwararrun masu tsaron gida ke neman hana Atiku cin bugun ‘fanaritin sa’ na ƙarshe.
Wannan jarida a baya ta yi sharhin cewa a yanzu dai ko yaro na goye a ƙasar nan ya kwana da sanin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar na cikin gagarimar matsalar da za a iya cewa ya janyo wa kan sa, tun bayan da ya yi gaban-gabarar watsi da shawarwarin manyan jam’iyya, ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Kusan gaba ɗayan manyan ƙusoshin jam’iyyar PDP sun cika da mamakin yadda Atiku ya yi watsi da shawarar da kwamitin fidda mataimakin shugaban ƙasa ya ba shi, cewa Gwamna Nyesom Wike ne na Jihar Ribas ya fi dacewa da kuma cancanta Atiku ya ɗauka takarar mataimaki.
Atiku ya hamɓare kwandon shawarar da aka ba shi, bayan da ya yi masu alwashin cewa zai yi aiki da shawarar ta su, ya ɗauki Okowa, ba tare da tuntuɓar su, ko sanar da su dalili ba.
Raddin Gwamna Ortom Kan Atiku: Ba Ni Da Tabbacin Zan Goyi Bayan Atiku A Zaɓen 2023:
Shugaban kwamitin mutum 17 da PDP ta kafa domin fitar wa Atiku Abubakar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, wato Samuel Ortom na Jihar Benuwai, ya fusata da yadda Atiku ya yi watsi da shawarar da su ka ba shi, inda ya ɗauki Ifeanyi Okowa a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, maimakon Gwamna Nyesom Wike da su ka rattaba, su ka miƙa masa sunan sa.
Cikin wata tattaunawa da ARISE TV ta yi da Ortom a wannan makon, ya ce Atiku ya baɗa masu ƙasa a ido, ya yi watsi da matsayar da su ka ɗauka.
Wani ƙarin haushi a cewar Ortom shi ne yadda Atiku har yau bai tuntuɓi Wike ya ba shi haƙuri ba, kuma Atiku bai shaida wa kwamiti dalilin sa na ƙin ɗaukar Wike ba.
A kan haka ne Ortom ya ce shi fa a yanzu dai haƙiƙa ya dawo daga rakiyar Atiku, hankalin sa bai kwanta cewa zai goyi bayan zaɓen sa a 2023.
“Ba na jin zan goyi bayan takarar Atiku, amma dai zan ci gaba da yin addu’a idan Ubangiji na ya ƙaddare ni da mara wa Atiku baya, to shikenan sai na yi haka ɗin. Amma dai har yanzu kam ya fita daga harkokin gaba na.”
Ɗan Kudu Mu Ke So A Ba Takara, Ba Atiku Ba -Ayo Fayose:
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya fito ƙarara ya ce Atiku ya ci amanar Wike, don haka ba zai goyi bayan kamfen ɗin sa ba.
Wata gagarimar rigima ta kunno kai a cikin Jam’iyyar PDP, inda tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya bayyana cewa Gwamna Nyesom Wike na Rivers da magoya bayan sa kakaf ba za su goya wa Atiku Abubakar baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba.
A cikin wata tattaunawar musamman da Fayose ya yi da PREMIUM TIMES, Fayose ya ƙara jaddada cewa tabbas Atiku ya ci amanar Wike, don haka Wike da jama’ar sa za su zuba wa Atiku Ido, “tunda ya na ganin cewa shi kaɗai zai iya cin zaɓe, sai ya je ya ci ɗin.”
Fayose ya ce, “bayan Atiku ya yi nasara a zaɓen fidda-gwani, ya je har gida ya nemi haɗin kan Gwamna Wike, kuma ya yi masa alƙawarin zai naɗa shi ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
“Kuma da aka kafa kwamitin tuntuɓa wanda zai fito wa Atiku da ɗan takarar mataimaki, kwamitin ya bayar da sunan Wike.
“Amma da aka shiga aka fita, sai Atiku ya wancakalar da Wike, ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta.
“Atiku bai yi wa Wike mutunci ba. Domin bayan ya ci amanar sa ya ƙi ɗaukar sa mataimaki, ai ya-kamata ya kira Wike ya sanar da shi dalilin da ya sa ya karya alƙawarin da ya yi, wato ya ba shi haƙuri, amma Atiku bai yi hakan ba.”
Fayose ya ce har yau ya na na nan kan ra’ayin sa cewa kudu ya kamata ya yi mulki ya koma kudu a 2023.
“Yan Arewa na ganin Goodluck Jonathan bai kamata ya ci zangon ‘Yar’Adua daga 2015 zuwa 2019 ba. Saboda haka sai su ka kori Jonathan ta hanyar zaɓen Buhari a ƙarƙashin APC.
“To tunda Buhari ya kammala shekarun sa takwas, ya kamata a yi adalci a bai wa ɗan kudu mulki, ba wai a ce Atiku ne daga Arewa zai fito neman zama shugaban ƙasa ba.
“Ni ina da tabbacin cewa ko kamfen Wike ba zai taya Atiku ba. Mu da ke goyon bayan Wike, duk wanda ya ce mu zaɓa shi za mu zaɓa, amma ba zai taɓa cewa mu zaɓi Atiku ba.”
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran Atiku, mai suna Paul Ibe. Ya ce ya kamata a daina gunguni da ƙulafuci, a haɗa kai a yi nasara, a kori APC.
Zafin Duka Da Gudumar Da Obasanjo Ya Yi Wa Atiku Bai Daina Yi Masa Raɗaɗi Ba:
CIkin makon jiya ne tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a rayuwar sa ya tafka manyan kura-kurai biyu.
Ɗaya daga cikin manyan kura-kurai biyu da ya ce ya yi a rayuwar sa, shi ne ɗaukar da ya yi wa Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a lokacin takarar zaɓen 1999.
Wannan kalami tabbas bai yi wa Atiku daɗi ba, wanda a yanzu haka ya lula Dubai ya bulaguro a can.
Kaushin da haushin wannan kalamin ne ya sa Shugaban Dattawan PDP Walid Jubrin ya bai wa Obasanjo sa’o’i 48 cewa ko dai ya janye kalaman da ya yi kan Atiku, ko kuma Jubril ɗin shi ma ya fallasa Obasanjo, duniya ta ji wani mummunan aibi kan sa.
Har ila yau Atiku na shan suka kan zarge-zargen baya da aka sha yi masa musamman wajen wai da hannun sa a afkuwar wasu manyan matsalolin ƙasar nan, musamman sayar da wasu kamfanonin gwamnatin tarayya a lokacin da ya na mataimakin shugaban ƙasa.
Sannan kuma duk da rashin farin jinin da APC ke fama da shi a yanzu bayan ta shafe shekaru bakwai kan mulki, tare da kasa magance matsalolin ƙasar nan, ba a daina yi wa PDP kallon musabbabin haddasa matsalolin a shekaru 16 ɗin da ta yi ta na mulki tsakanin 1999 zuwa 2015 ba.
Discussion about this post