Kotun Koli ta saurari Lauyoyin mgwamnonin da suka kai karar gwamnatin tarayya da babban bankin Kasa CBN, da suke kalubalantar wa’adin kashe takardun kuɗi da ka canja launin su a kasar nan.
Lauyoyi sun tattauna a zauren kotun kolin inda manyan alkalai su 7 na kotun kolin suka saurare su.
Ba ya ga jihohi 10 da ke adawa da kuma ƙalubalantar wannan tsari na gwamnatin tarayya, akwai jihohi kamar su Bayelsa da ke goyon bayan gwamnati da babban bankin Najeriya, CBN.
Bayan mahawarar da aka yi, babban alkali John Okoro a madadin sauran alkalan ya ce an dage zaman kotun zuwa 3 ga Maris domin yanke hukunci akan takaddamar.
Idan ba a manta ba, gwamnonin akalla 10 da suka hada da Kaduna, Jigawa, Kano, Kogi da sauran su sun maka gwamnatin tarayya da CBN, suna kalubalantar canjin fasalin takardun naira da gwamnati ta yi
A dalilin wannan canji, an jefa ƴan kasa cikin ruɗani da halin ƙaƙanikayi a dalilin rashin kaiwa ga kuɗaɗen su.
A jihohin Ogun da Ondo, hasalallun matasa sun kona wasu manyan bankuna da lalata na’urorin ATM.
Discussion about this post