Ɗan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi, ya lashe ƙ
Ƙaramar Hukumar Alimosho, ƙaramar hukuma mafi yawan masu jefa ƙuri’a a Jihar Legas.
Peter Obi ya lashi ƙuri’u 71,327, ahi kuma Tinubu 62,909. Atiku Abubakar na PDP kuma 8,201.
Zuwa yanzu Tinubu ya ci ƙananan hukumomi 11, Peter Obi kuma 8.
Har yau a Legas, ‘yan takarar LP biyu sun kayar da mawaƙi Banky W da ɗan Sanata Obanikoro a zaɓen Majalisar Tarayya.
Can a Jihar Filato ma Peter Obi ya fara jijjiga APC da PDP tun kafin a kammala ƙirga ƙuri’u.
Ɗan takarar LP Peter Obi, ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi 6 a cikin 8 da aka bayyana sakamakon zaɓen su. Yayin da PDP kuma ta lashe ƙananan hukumomi biyu.
Akwai dai ƙananan hukumomi 17 a Jihar Filato, inda a yanzu ake jiran sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 9 kenan.
Obi ya lashe Langtang North, Barikin Ladi, Riyom, Jos East, Mangu da Bakkos.
Shi kuwa Atiku na PDP ya lashe Langtang ta Kudu da kuma Mikang.
LP ta samu 32,489 a Barikin Ladi, Riyom kuma 15,171, Jos East 6,386, Langtang North 21,590, Bakkos 32,581. Mangu kuma 39,387.
A Jihar Nasarawa an sake lallasa Shugaban APC, SDP ta lashe kujerar Sanatan Nasarawa na Shiyyar Abdullahi Adamu.
Ahmed Wadada na jam’iyyar SDP ne ya yi nasarar lashe kujerar Sanatan Shiyyar Nasarawa ta Yamma, Mazaɓar Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu.
Wadada ya samu ƙuri’u 96,488, ɗan takarar APC kuma ya samu 47,717.
Wanda ya zo na uku shi ne Galadima Musa na PDP da ƙuri’u 46,820. LP ta samu 33,228.
A Jihar Katsina kuwa Ƙanin Umaru ‘Yar’Adua, Abdu Soja ya lashe kujerar Sanatan Katsina Tsakiya.
Ɗan takarar Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdul’aziz Yar’Adua na APC ne ya yi nasarar lashe zaɓen a jihar Katsina, inda ya samu ƙuri’u 153,512. Na PDP Aminu Sirajo kuwa ya samu 152,140.
Abdul’aziz tsohon Laftanar Kanar ne mai ritaya. Shi ne ya maye gurbin Sanata Kabir Barkiya, wanda ya sha kaye tun a zaɓen fidda gwani.
Wani sakamako daga jihar Gombe kuma ya nuna Atiku ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Gombe, ya nunka Tinubu samun ƙuri’un jihar.
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Jihar Gombe 11.
Baturiyar Zaɓe Farfesa Maimuma Waziri ta bayyana Atiku ya samu ƙuri’u 319,123, shi kuma Bola Tinubu na APC ya samu 146,977.
A Ƙaramar Hukumar Gombe ce Atiku ya fi samun yawan ƙuri’u har 62,347, sai Akko 55,202, sai kuma Yamaltu Deba 38,479.