Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa cikin kwanaki bakwai din da suka rage da ƙarin wa’adin canja tsoffin takardun kuɗi zan maida hankali a kawo ƙarshen wahalar da talakawa ke ciki.
Waɗannan sune kalaman da Buhari ya yi wa gwamnonin APC da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa ranar Juma’a.
” Zan kira babban bankin kasa, da kuma kamfanin buga kuɗi na kasa domin a san yadda za a kawo karshen wannan matsala kuma cikin sauran kwanaki bakwai din da suka rage.
Gwamnonin sun shaida wa Buhari cewa, lallai suna goyon bayan wannan magana na canja kuɗi matuka, sai dai kuma wasu sun yi wa abin shigo-shigo ba zurfi suna kokarin rikirkita tsarin da hakan ya sa talakawa a jihohin su ke fama da tsananin wahala saboda rashin isassun takardun kuɗi.
Sun roki shugaban kasa ya saka baki, a ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin kuɗin har zuwa karshen shekara, zuwa nan an saba kuma sabbin kuɗin ya wadatu.
A karshe shugaba Buhari ya ce ya saurari gwamnonin kuma lallai daga wurin sa zai tabbatar an yi wani abu na gaggauwa domin a warware matsalar ƙarancin kuɗin a fadin kasar nan.
Idan ba a manta ba , gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai a hira da ya yi da talbijin ɗin Channels ya ce wasu makusantan Buhari ne suka kirkiro wannan matsala domin kawai kada ɗan takarar shugaban kasa, na APC yayi nasara a zaben shugaban kasa
Discussion about this post