‘Yan Najeriya na ta kwarara wa gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara addu’o’in fatan alkhairi kan nasarar da suka samu a Kotun koli bisa babban bankin Nageriya kan janye lokacin da za adaina karbar tsoffin kudi a Najeriya.
Idan ba a manta ba, gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da takwarorin sa na Kogi, Yahaya Bello, da na Zamfara, Bello Matawalle sun kai karar babban bankin Najeriya kotun Koli domin kotu ta tilasta mata ta dakatar da ranar da za a dakatar da amfani da tsoffin kudi a kasar nan.
Babban kotun ta yanke hukuncin dakatar da wannan shiri da CBN ta tsara, ta ce za a ci gaba da sauraren shari’ar ranar 15 ga Faburairu.
Hakan na nuna cewa za a ci gaba da karba da kasuwanci da wadannan kudade har sai bayan kotun Koli ta yanke hukunci.
Bisa wannan dalili, yan Najeriya da dama sun rika tofa albarkacin bakin su game da hakan.
Gambo Lawal wanda mazaunin Kaduna ne ya bayyana cewa lallai akwai wadannan gwamnoni sun cancanci yabo matuka, domin wannan jihadi ne suka yi wa talakawa.
” Tsakani da Allah wannan kamar jihadi ne gwamnonin nan uku suka yi bisa jagorancin gwamna El-Rufai. Mutane sun shiga cikin tsananin mawuyacin hali da kudin su amma samun su ya gagare su. Amma matsin da su kayi har suka je Kotu aka samu wannan hukunci yayi mana dadi.
” Ko ma dai siyasa ce suka yi mu dai aii ya amfane mu. Da yaya za mu yi da sauran kudaden mu da muke kasuwanci da su.
Hawwa Balarabe, ta ce ” Shi abu lokacin da aka yi shi shine yake amfanar mutane. Ko ma menene, kwanakin nann da za ayi zai taimaka mutane su samu kudade a hannun su.
Da yawa mutane na ci gaba da kukan cewa kudaden sun yi karanci.
A jawabin da El-Rufai yayi wa ‘yan Kasuwan Kaduna ranar Talata ya ce kada mutane su ci gaba da fargaban kudaden su. Idan Bola Tinubu na APC ya ci zabe zai dakatar da maganan canja kudin. za a bi abin cikin natswa sai kowa ya wadatu da sabbin sannan a hankali kuma a janye tsoffin takardun kudin ba a ma sani ba.