Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nassrorin dalilin sauya launin kuɗi sun fara bayyana, duk kuwa da ƙorafe-ƙorafen halin ƙuncin da jama’a su ka shiga na ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
Buhari ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa na ranar Alhamis, wanda ya yi wa ‘yan Najeriya, inda ya bayyana damuwa dangane da halin da aka shiga, a gefe ɗaya kuma ya ke jinjina wa nasarorin da ya ce sauya launin kuɗin sun fara samarwa.
Buhari ya yi wannan bayani daidai lokacin da tuni wasu hasalallun matasa sun fara fusata a garuruwa daban-daban, su na banka wa bankunan kasuwanci wuta.
“An shaida min cewa daga lokacin da aka shigo da sabbin kuɗi zuwa yau, naira tiriliyan 2.1 da ake damfare a hannun mutane an mayar da su banki. Wannan kuma babbar nasara ce.”
Buhari ya ce ba zai yiwu a rage tsadar rayuwa ba har sai an rage kuɗaɗen da ke shige-da-fice a hannun jama’a tukunna.
Sannan kuma ya ce sabon tsarin ya daƙile yawancin ayyukan ɓarnar da ake yi ta hanyar tara maƙudan kuɗaɗe ta hanyar da doka ta yi hani a kai.
Domin a samar wa jama’a sauƙin hada-hada, Buhari ya umarci CBN ta halasta karɓar tsoffin naira 200 har tsawon watanni biyu, wato zuwa 10 Ga Afrilu.