Ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya roƙi ‘yan Najeriya su kai zuciya nesa, yayin da Gwamnatin Tarayya da sauran jami’ai ke ƙoƙarin shawo kan gagarimar matsalar
Tinubu ya yi wannan roƙon a lokacin a Abuja ranar Talata, lokacin da ya ke tausaya wa jama’a, musamman marasa galihu, waɗanda su wannan kujiba-kujiba ta fi shafa.
Ya ce a yi haƙuri da wannan matsananciyar wahalar canjin sabbin kuɗi da ƙarancin fetur su ka fi shafa.
Duk da ƙarin kwanaki 10 da CBN ya yi, har yanzu ana tsakiyar wahalar, lamarin da har ta kai ana zanga-zanga da tarzoma a faɗin ƙasar nan.
Tinubu a baya lokacin kamfen a Abeokuta, ya yi zargin cewa an ƙirƙiro matsalar fetur da canjin kuɗi lokacin zaɓe ne don a hana shi yin nasara.
A farkon wannan makon ne dai kotu ta umarci CBN kada ya wuce wa’adin 10 Ga Fabrairu.
Babbar Kotun Tarayya da ke Wuse Zone 2, Abuja, ta umarci Babban Bankin Najeriya CBN cewa ya tabbatar bai ƙara ko kwana ɗaya daga ranar 10 Ga Fabrairu na wa’adin daina amfani da tsoffin kuɗaɗen naira ba.
Mai Shari’a Eleojo Enenche ne ya bayar da wannan hukunci a ranar Litinin, a ƙarar da wasu jam”iyyun siyasa huɗu su ka kai CBN kotu.
Jam’iyyu huɗu da su ka ƙunshi AA, APP, APM da NRM sun shigar da ƙara cewa bankunan kasuwanci ne ke wa sabon tsarin canjin kuɗi ƙafar ungulu.
Sun kai Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya da wasu bankuna 25 ƙara kotu.
Kotu ta umarci Buhari, CBN, Gwamnan CBN da bankuna 25 kada su ƙara wa’adi daga ranar 10 Ga Fabrairu, har sai kotu ta kammala sauraren ƙorafin jam’iyyun huɗu tukunna.
Kotun kuma ta aika wa bankunan 25 sammacin su je su yi bayanin dalilin da ya sa ba za a gurfanar da su ba, saboda sun kawo zagon ƙasa, ta hanyar ɓoye sabbin kuɗaɗe, sun ƙi bai wa kwastomomi sabbin naira 200, naira 500 da naira 1,000.”
A ranar Litinin EFCC ta bayyana damƙe wani manajan banki, saboda ya danƙare maƙudan sabbin kuɗaɗe, ya ƙi bai wa kwastomomi.
Sai dai kuma EFCC ba ta ambaci sunan sa ko sunan bankin sa manajan ke aiki ba.
Wannan umarni na Babbar Kotun Tarayya ya zo ne bayan Gwamnonin APC uku sun garzaya Kotun Ƙoli, sun shigar da ƙara cewa wa’adin ranar 10 Ga Fabrairu da za a daina karɓar tsoffin kuɗaɗe ya yi kaɗan.
Gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara ne su ka garzaya kotun, su na buga misali da irin baƙar wahalar da ‘yan Najeriya ke sha, sakamakon ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
Tinubu ya ce duk abin da za a yi a riƙa tunawa da talakawa, waɗanda su ne irin wannan matsala ta fi shafa.
Ya roƙi jama’a su guji ɗaukar doka a hannun su, ya ce nan ba da daɗewa ba komai zai warware.