Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ‘doka ribas’ kan goyon bayan da ya baiwa kan canjin launin takardun kuɗi da gwamnatin Buhari ta yi, yanzu ya lashe aman sa, ya ce ba a yi wa talaka adalci ba.
Idan ba a manta ba, a baya, Atiku ne a kan gaba wajen yabawa da jinina wa gwamnatin Buhari kan bijiro da canjin takardun naira 200, 500 da 1000 da babban bankin kasar CBN ta yi.
Atiku ya ce yana goyon bayan shirin kuma ya yi kira da rokon gwamnati a lokacin da kada su canja wannan tsari ko kara wa’adin da aka baiwa mutane su sauya kuɗaɗen su zuwa sabbi
Ya rika cewa gwamnati ta yi daidai abinda ta yi duk da bakar wahalar da mutane suka afka ciki a kasar sanadiyyar wannan canjin kudin.
Gwamnonin APC da manyan jigajigan jam’iyyar sun fito karara don nuna adawar su ga wannan canja launin kuɗi da gwamnati ta bijiro da shi a daidai lokacin zaɓe da mutane za su bukaci kuɗaɗe don hidimomin su.
Gwamnatocin sun maka gwamnatin tarayya da CBN a kotu suna kalubalantar wannan tsari da ake sa ran za a yanke hukunci ranar laraba mai suwa.
A sakon da Atiku ya fitar wanda ya rubuta a shafinsa na Facebook, Atiku ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta dakatar da wannan shiri ta kuma kyale bankuna su rika karbar tsoffin kuɗi a hannun mutane.
Ya yi kira da a yi sassauci ga maganar sauya launin takardun kudin saboda irin kuncin da talakawa suka shiga a faɗin kasar nan.