Ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana cewa tsarin sauya launin kuɗi ya tsiyata dukka ƴan Najeriya ne da ‘yan takarar shugaban ƙasa 18 ƙarƙaf.
Kwankwaso ya ce a yanzu shi da sauran ‘yan takarar da ke masa kallon ba shi da kuɗi, sun dawo daidai. Don haka yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa zai yi masa sauƙi.
Kwankwaso ya yi wannan bayani lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan rediyon Dandal Kura, Maiduguri jihar Barno.
Ya ce masu yi masa shegantaka wai ba shi da kuɗi, ɗin haka me zai sa ya shiga takarar shugaban ƙasa, su ma yanzu ba kuɗin gare su ba.
Ya ce tsarin canja kuɗi ya talauta kowa, har da manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa baki ɗaya.
“Mun sha jin mutane su na gwasale mu, wai Rabi’u Kwankwaso ba shi da kuɗin da zai yi kamfen. To a yau dai duk shugaban ƙasa ya maida kowane ɗan takara matalauci. To yanzu dai kowane ɗan takara ya koma talaka kamar ni kenan.”
Kwankwaso ya ce irin muhimman ayyukan da ya gudanar a jihar Kano lokacin da ya yi gwamna sau biyu sun zama ma’aunin cancantar sa. Kuma ya bada bayanin kasancewar sa ya yi ministan tsaro kuma ya yi sanata.
Ya ce kada ‘yan Najeriya su sake yin gangancin zaɓen APC da PDP, saboda ba su da wani abin da za su yi wa ‘yan Najeriya romon-kunne da shi kuma.
A baya Kwankwaso ya ce bai yarda an ƙirƙiro canjin kuɗi don a kayar da ɗan takarar APC, Bola Tinubu ba. Ya ce Tinubu na hargagin tsoron faɗuwa zaɓe ne kawai.