Kakakin kungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa canja launin takardun kuɗi da gwamnatin Buhari ta bijiro da shi hanya ce kawai ta gogawa jam’iyyar APC baki jini mutane su goje ta.
A hira da yayi da talbijin ɗin Channels, Baba-Ahmed ya ce ko makiyin APC na gani kasheni ba zai kulla mata irin wannan tuggun ba da sunan wai gyara kasa a jajibarin zaɓen shugaban kasa, da zumman kuma wai jam’iyyar na so ta yi nasara a zaɓe.
A cewarsa, da alama shugaban kasa Muhammadu Buhari baya sauraron kowa duk da cewa zai iya kawo karshen matsalar ta hanyar barin kuɗaɗen biyu suyi aiki kafada da kafada, wato arika kashe tare har zuwa wani lokaci da sabbin kuɗin za su wadatu.
“ Ƴan APC ɗin da kansu na cewa an fito da wannan sha’ani na canja kuɗi ne don jam’iyyar ta sha kasa a zaɓe mai zuwa, haka suma gwamnonin APC ɗin har da shi kansa ɗan takarar shugaban kasan, Bola Tinubu.
” Mutanen kasa sun afka cikin tsananin wahala, a cikin makonni hudu kacal ya gurgunta tattalin arzikin kasa, ya dagula kasa, ya birkita komai kuma yayi shiru tsit, shi bai iya hana Emefiele ba sannan kuma bai bari a ci gaba da kashe tsoffin kuɗaɗen ba.
” Ai ko makiyin APC ba zai bijiro da iri wannan bala’i ba a daidai jajibarin babban zaɓe, sanna Buhari na kamfen wai azaɓi jam’iyyar a irin wannan bakar wahalar da mutane ke ciki. Shi ko wani irin mutum ne?
A karshe Baba-Ahmed ya ce har yanzu kungiyar bata sanar da ɗan takarar ta ba cikin masu neman shugaban kasa a zaɓe mai zuwa. Sai dai ya ce nan ba da dadewa ba za su sanar da ɗan takarar su.
Discussion about this post