Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya nuna rashin jin dadin sa game da yadda shugaban Kasa Muhammadu Buhari dakile farin jinin APC a kasar nan sannan kuma ya na kokarin tarwatsa Dimokuradiyya a kasar nan.
Ganduje, wanda na hannun daman dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ne, Bola Tinubu, ya yi wannan ikirari a wata ganawa da kungiyar tsaffin ‘yan majalisar tarayya daga yankin Arewa maso Yamma a ranar Laraba.
Gwamnan Ganduje na Kano wacce ita cecibiyar kasuwancin arewacin Najeriya ya ce kamata ya yi a bijiro da wannan shiri na canja kudi shekaru bakwai da suka gabata ko kuma bayan zabe amma ba yanzu ba.
Gwamnan ya kara da cewa bijiro da wannan canja takardun kudi da Buhari ya yi zai ruguza jam’iyyar da ya zama shugaban kasa a karkashinta na wa’adi biyu a jere.
” Tsakani da Allah ku dubi wannan mutumin da ya yi shekaru da dama yana neman mulkin Najeriya amma bai samu ba, sai da aka yi hadin guiwa aka yi maja sannan Allah ya bashi nasara. Ya sake dawowa a karo na Biyu a karkashin Jam’iyyar ya kuma yi nasara amma yanzu da gangar tunda ya samu abinda yake so yana so ya ruguza jam’iyyar ya kama gaban sa. Tsakani da Allah yaya mutum zai yi irin haka.
“ Sai yanzu da lokaci ya yi da za a yi zabe sai ku kawo wannan tsari, don Allah me ya sa wannan sai a wannan lokaci, meye amfanin yin ta a yanzu? Me zai hana bayan zabe? Me ya sa ba a yi wasu shekaru bakwai a baya ba? Duk wani dan siyasa zai tambayi wannan: menene alfanun wannan abu? Gwamnan CBN bai fahimci wadannan abubuwa ba, shi ba dan siyasa ba ne.
Shi kanshi bankin duniya ya ce wannan abu da gwamnatin Najeriya ta bijirodashi ba kamata ayi shi a wannan lokaci ba, IMF ma haka, shugabannin kasashen duniy suma sun ce hakan bai dace ba amma ya ki yin komai a kai.