Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicin yadda mace ɗaya tilo ce ke takarar gwamna a zaɓen 2023.
Dangane da hakan sai ya ce ya na goyon bayan A’isha Binani 100 bisa 100, a takarar da tacke yi ta gwamnan Jihar Adamawa.
Da ya ke jawabi bayan ya jefa ƙuri’a a Daura, Buhari ya ce ya ɗaga ƙuri’ar sa sama kowa ya shaida Bola Tinubu na APC ya ke goyon baya.
Ya ce kalaman sa da ayyukan sa sun sha nuna cewa Tinubu ya ke goyon baya, kuma har yau bai canja ba. Saboda haka ya yi kira a zaɓe shi, tare da cewa ya na da yaƙinin Tinubu ɗin ne zai lashe zaɓe, “tun daga Katsina har Legas arankatakaf.”
Wannan ne karo na farko da babu sunan Muhammadu Buhari a cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa, tun daga 2003 har zuwa yau tsawon shekaru 20.
Buhari ya jefa ƙuri’a tare da matar sa A’isha Buhari a Daura, jihar Katsina.
Wannan jarida ta buga labarin kama matasa 15 da kwamfutoci, ana zargin su da niyyar kutsen baddala sakamakon zaɓe a Katsina.
A Jihar Katsina Rundunar ‘Yan Sanda ta damƙe wasu matasa 15 da aka samu tare da sabbin kwamfutoci.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES kama matasan.
Sai dai ya ce ba gaskiya ba ne da ake yaɗa cewa an kama su da tulin ƙuri’u.
Ya ce an kama su da kwamfutoci laptop, waɗanda ake masu zargin cewa za su kutsa ne domin leƙen sakamakon zaɓe ko kuma baddala sakamakon.
Wata majiya ta bayyana wa wakilin mu cewa dukkan kwamfutocin da jami’an tsaron su ka kama a hannun matasan akwai tambarin wata jam’iyyar siyasa jikin ta.
Discussion about this post