Kotun Ƙoli ta ƙwace takarar gwamnan Jihar Taraba daga hannun Sanata Emmanual Bwacha na APC, bisa hujjar cewa APC ba zaɓi Bwacha a ƙarƙashin halastaccen zaɓen fidda gwani ba.
A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba, Alkalai biyar ne su ka zauna su ka yanke hukuncin, a ƙarƙashin Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, waɗanda su ka amince da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo ta yanke a baya.
Kotun ta yarda da cewa APC ba ta gudanar da halastaccen zaɓen fidda gwanin ɗan takara ba a lokacin da aka tsayar da Bwacha.
Wani wanda ya yi takara da Bwacha ne mai suna David Kante ya fara shigar da ƙarar da ya ƙalubalanci tsayar da Bwacha a ƙarƙashin APC.
Daga nan ne a ranar 20 Ga Satumba, 2022 Mai Shari’a Simon Amobeda na Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo ya soke takarar Bwacha.
Mai Shari’a ya gamsu da cewa a filin jirgin sama aka rikodin ɗin cewa Bwacha ne ya yi nasara a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaɓen fidda gwani na APC.
A ranar 24 Ga Satumba, 2022, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Yola ta maida Bwacha a matsayin ɗan takarar gwamna a Taraba na APC.
Daga nan ne Kante ya fusata ya kantara a guje zuwa Kotun Ƙoli, domin a bi masa haƙƙin sa. Ya shigar da ƙara a Kotun Ƙoli ta hannun lauya Kanu Agaji.
Cikin watan Nuwamba ne kotu ta ƙwace kujerar Sanata Bwacha, saboda ya canja sheƙa daga PDP ya koma APC.
Babbar Kotun Tarayya da ke Jalingo babban birnin Jihar Taraba, ta umarci Sanata Emmanual Bwacha da ya gaggauta ficewa daga Majalisar Dattawa saboda ya sauya shaƙa daga jam’iyyar da ta zaɓe shi wato PDP, ya koma APC.
Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya ɗin ya an zaɓi Bwacha ne a ƙarƙashin PDP, don haka ya sauka ya bar wa PDP kujerar sanatan da ya ke a kai, ya ci gaba da zaman sa a APC ɗin da ya koma.
Da ya ke yanke hukunci a ranar Juma’a, ya ce ba zai yiwu haka kawai wasu ‘yan jam’iyya su sha wahalar zaɓen ka, sannan daga baya ka tsallake ka bar su ka koma wata jam’iyya ba.
Mai Shari’a ɗin ya ce yanzu PDP na da damar da za ta maye gurbin Bwacha. Sai dai kuma har yau Sanata Bwacha bai ce komai dangane da wannan hukunci da kotu ta yanke a kan sa ba.
Dama kuma cikin Satumba 2022 kotu ta ƙwace takarar gwamnan Jihar Taraba na APC daga hannun Bwacha.
Bayan ya yi nasara a zaɓen fidda gwani, an kai ƙara kotu, inda kotu ta tabbatar da cewa ba a gudanar da zaɓen fidda-gwanin da Bwacha ya yi nasara bisa ƙa’ida ba.