Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada wa Gwamnonin APC cewa ba zai yi wa zaɓen 2023 katsalandan ba.
Ya yi masu wannan bayani ne a ranar Juma’a, lokacin da su ka kai masa ziyara, domin su nuna masa halin da ƙasar nan ke ciki sanadiyyar sauya launin kuɗi.
Da ya ke masu jawabi, Buhari ya kafa masu hujja da buga misalai da cewa:
“Mun tabbatar kuma mun ga abin da ya faru a zaɓukan Anambra, Ekiti da Osun. Abin da ya faru a waɗannan jihohi ya ƙara min ƙwarin guiwar cewa mu na samun gagarimar nasara.”
Da ya koma maganar wahalhalun da jama’a ke sha, ya roƙi ‘yan Najeriya su ba shi wa’adin mako ɗaya domin ya shawo kan matsalar ƙarancin sabbin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Ya ce maƙasudin kafa sabon tsarin hada-hadar kuɗaɗen ba don a ƙaƙaba wa jama’a wahala ba ce, sai don a sauƙaƙa wa mutane rayuwa ta hanyar tasarifin kuɗaɗe a sauƙaƙe.
Sai dai kuma ya zargi wasu bankuna da laifin kawo cikas a lamarin, inda ya ce “wasu bankunan ba su da babban jari sosai, saboda haka kan su kawai su ka sani.”
Buhari ya ce ya nuna damuwa ganin yadda ya kalli fayafayen bidiyon yadda mutane ke wahala a bankuna wurin ƙoƙarin cirar kuɗi a cikin bankuna a kuma a na’urar ATM.
Ya ce zai gana da CBN da kuma Kamfanin Buga Kuɗaɗe na Najeriya domin a fuskanci gaskiyar lamarin.
Sai dai kuma duk da gwamnonin sun nuna wa Buhari goyon bayan sabon tsarin da kuma sauya launin kuɗaɗe, sun nuna masa irin halin da jama’a su ka tsinci kan su sakamakon canjin kuɗaɗen.
Sun nuna masa tsoron cewa wahalar da jama’a ke ciki za ta iya shafar nasarar jam’iyyar su a zaɓen 2023.
Daga nan Gwamnonin sun roƙi Buhari ya yi magana a wadata bankuna da sabbin kuɗaɗe, kuma a ci gaba da karɓar tsoffin ana hada-hada da su, daga nan har ƙarshen shekara.
Buhari ya ce kafin a fara buga kuɗin, ya ce kada a sake a buga su a ƙasar waje, sai dai a buga a cikin Najeriya. Ya ce an kuma tabbatar masa cewa za a iya buga wadatattu a cikin ƙasar nan.
A ƙarshe ya ce dalili kenan zai zauna da CBN da Kamfanin Buga Kuɗi domin ya gano gaskiyar lamarin.