Kimanin mutum 10, ne su ka rasa rayukan su sakamakon mummunar girgizar ƙasa da ake fuskanta a ƙasashen Turkiyya da Siriya.
Kwanaki uku kenan dai a jere ƙasashen biyu ke fuskantar wannan bala’i, wanda ya ci rayuka 7,108 a Turkiyya, sai wasu 2,530 a Siriya.
Shugaba Turkiyya Racep Erdogan zai ziyarci kudancin ƙasar inda girgizar ta yi muni sosai.
Sannan kuma ya zartas da dokar ta-ɓaci a yankuna 10 ɗin da girgizar ta shafa.
Ana ci gaba da aika wa Turkiyya da goyon baya ciki har da jami’an ceton rayuka.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda a cikin kwana ɗayan farko girgizar ƙasar ta ci rayukan mutum kusan 5,000 a Siriya da Turkiyya.
Aƙalla an yi asarar rayukan mutum 4,800 tare da wasu dubban mutanen da su ka ji munanan raunuka, sanadiyyar mummunar girgizar ƙasa a garuruwan da ke kan iyakar Siriya da Turkiyya.
Jami’in Hukumar Kai Agajin Gaggawa (AFAD), ya ce waɗanda su ka rasa rayukan su a Turkiyya zuwa wayewar garin ranar Talata, za su kai 3,381. Ya ce kimanin mutum 20,426 sun ji raunuka.
Tatar ya ce girgizar ƙasar dai a Turkiyya ta ruguza gidaje kantama-kantama guda 5,700.
A Siriya kuwa an samu rahoton da ya tabbatar da cewa girgizar ƙasa ta kashe mutum 1,444, wasu 3,500 sun ji raunuka, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Ilmi ta Siriya ce ta bada sanarwar adadin waɗanda su ka mutum da waɗanda su ka jikkata ɗin.
Aljazeera ta ruwaito Shugaban Turkiyya Racep Erdogan na cewa girgizar ƙasar guda biyu da aka yi a ranar “ita ce babba mafi muni” tun bayan wadda aka yi a cikin 1939, wadda ta kashe mutum 33,000.
Erdogan ya bada hutun mako guda domin yin jimami, ita kuma Siriya ta nemi taimako daga Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaggauta kai mata agaji.
Ƙasashe da dama ciki har da Najeriya sun aika da saƙon jimamin rashin dubban mamatan.