Ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya shawarci Babban Bankin Najeriya (CBN), kada ya ƙara wa’adin karɓar tsoffin kuɗaɗe, bayan kwanaki goma ɗin da bankin ya bayar zuwa 10 Ga Fabrairu.
Cikin wata sanarwa da Atiku ya fitar ranar Laraba a Abuja, ya ce ƙarin wasu wa’adin kwanaki zai dagula maƙasudin sauya wa kuɗaɗen launi ɗungurugum.
“Ƙarin kwanaki 10 zai bai wa ‘yan uwan mu da ke karkara damar jidar kuɗaɗen su daga gidaje su kai su bankuna.
“Yin hakan kuma zai bai wa CBN damar rarraba sabbin kuɗaɗe zuwa bankuna daban-daban, ta yadda jama’a za su samu sauƙin samun kuɗaɗen su cikin sauƙi.”
Sannan kuma ya shawarci CBN ya sake nazarin tsauraran matakan sakin kuɗaɗe a hannun jama’a.
Ya ce yin hakan zai sauƙaƙa wa jama’a ƙuncin rayuwar da ƙarancin kuɗaɗe ta haifar masu, musamman a yankunan karkara.
‘Yan Najeriya na ci gaba da ɗanɗana kuɗar ƙuncin ƙarancin sabbin kuɗaɗe musamman a cikin bankuna da kuma wurin masu hada-hadar P.O.S a faɗin ƙasar nan.
“A cikin waɗannan kwanaki goma ina roƙon Babban Banking Najeriya, CBN ya ƙirƙiro hanyoyi da dabarun sauƙaƙe wa al’umma ƙuncin rayuwar da su ka shiga dalilin sauya kuɗaɗe.”
“Idan ma ta kama CBN zai iya tilasta wa bankuna su yi aiki a ranakun Asabar da Lahadi, domin su magance matsalar ƙarancin kuɗaɗe, musamman a yankunan karkara, waɗanda su kuɗaɗen da su ke buƙata ba wani yawa gare su sosai ba.”
A ƙarshe ya gargaɗi CBN ya yi hattara da manyan da za su riƙa kukan a ƙara wa’adin tsoffin kuɗaɗe, don wata ɓoyayyar manufar su kawai.
Discussion about this post