Rundunar Kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso sun karyata rade-raɗin da ta fito daga ofishin ɗin Kamfen ɗin Atiku Abubakar na PDP cewa wai Kwankwaso zai janye wa Atiku.
Sakatariyar kwamitin kamfen ɗin Ƙwankwaso, Folashade Aliu, wacce ta maida wa rundunar Atiku martani ta ce ” Shi fa Atiku ɗan ruɗu ne kuma cike yake da farfaganda a al’amuran sa. Gaba daya ya ɗimautu da sai yayi mulkin Najeriya amma kuma babu abu guda ɗaya da zai nuna ya yi wa ƴan kasa a lokacin da ya samu dama.
” Kullum sai dai ya fito ya na ɓaɓatu ya yana nuna shine ya fi kowa iyawa, mulkin kawai yake so ta rufe masa ido.
” Kwankwaso da rundunarsa ba su janye wa kowa ba, kuma ba za su janye wa kowani ɗan takara a zaɓen shugaban kasa ba. Iya ruwa fidda kai kawai. Kwankwaso na nan daram.
” Da kwankwaso za a fafata a zaɓen Asabar kuma sha ne zai yi nasara domin gaba ɗaya a kasar nan jama’a sun gane cewa lallai shi limamin canji don talakawa ne.
” Takarar shugaban kasa na jinin Atiku, ya saba, kuma kamar yadda yake ta tsalle-tsallen takara, haka ake naka shi da kasa, amma bai daddara ba, yanzu ma haka zai sha kasa don shi ba boyayye bane a idanun ƴan Najeriya kowa ya san shi ya san taɓargazar da ya tafka.
Discussion about this post