Sakamakon zaɓen rumfar gwamnan jihar Gombe wanda malamin Zaɓe ya bayyana bayan an kammala ranar Asabar ya nuna Atiku Abubakar na PDP ne ya yi nasara a rumfar.
Atiku ya samu ƙuri’u 215 a wannan rumfa inda ya kada Bola Tinubu na APC da ya samu Kuri’u 186.
Micheal Thomas, ya kara da cewa Kwankwaso na NNPP ya samu Kuri’u 10 kacal sai kuma Peter Obi na LP da ya samu Kuri’u 4.
Sai dai kuma a rumfar zaɓe na gwamna Masarin Katsina, Atiku ya sha kayi ne. Kuri’un da Tinubu ya samu sun nunka na Atiku sau huɗu.
Tinubu ya samu Kuri’u 208, Atiku kuma kuri’u 54 kaxal.