Daga cikin tsare-tsaren da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ke yi idan ya ci zaɓen 2023, akwai buɗe kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar wadda ke kulle a kan iyakar Jihar Yobe da Nijar.
Atiku ya ce idan aka buɗe kan iyakar zai sauƙaƙa ƙuncin rayuwa kuma za’a samu sauƙin zirga-zirga da hada-hadar amfanin gona tsakanin mazauna yankunan ƙasashen biyu.
Atiku wanda shi ma ɗan Arewa maso Gabas ne, ya yi alƙawarin kawo zaman lafiya a Jihar Yobe.
Atiku ya yi wannan alwashin ranar Laraba a Damaturu, lokacin da ya ke jawabi a wurin kamfen.
Ya ce zai samar da kuɗaɗe ga matasa da mata domin su samu sana’o’in dogaro da kan su da iyalan su.
“Idan ku ka zaɓi PDP, zaman lafiya zai dawo a Jihar Yobe. Za mu tabbatar mun buɗe makarantu, domin yaran mu su ci gaba da zuwa makaranta.
“Kuma mun yi alƙawarin tallafa wa matasa da mata ta hanyar ba su jarin da za su yi sana’o’in dogaro da kan su, har su cimma nasara a rayuwar su.
A na sa jawabin, Shugaban PDP Iyorchia Ayu, ya yi zargin cewa gwamnatin APC ta jefa ‘yan Najeriya cikin mummunan halin ƙuncin rayuwa.
Idan ba a manta ba, yayin da Atiku ya je kamfen a Katsina, ya sha alwashin cewa ‘an daina bindige ɗan Najeriya saboda buhun shinkafa idan na ci zaɓen 2023’
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cewa daga ranar da aka rantsar da shi idan ya ci zaɓen 2023, to daga ranar za a daina kashe ‘yan Najeriya saboda sumogal ɗin buhun shinkafa.
Atiku ya sake yin alƙawarin cewa kuma daga ranar za a buɗe kan iyakokin Najeriya.
Rufe kan iyakokin Najeriya da aka yi tun kafin annobar korona har zuwa yau, ya haifar da tsananin ƙuncin rayuwa, musamman a jihar Katsina, inda jami’an kwastan su ka yi ƙaurin suna wajen bindige masu fasa-ƙwaurin buhunan shinkafar da su ke shigowa da shi ta kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wani alƙawari da Atiku ya ƙara yi a gaban dandazon magoya bayan PDP, a filin wasa na Muhammad Dikko da ke Katsina, shi ne alkawarin magance matsalar tsaro da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Jihar Katsina na sahun gaba a jerin jihohin da ‘yan bindiga ke ci gaba da ragargazar su babu ƙaƙƙautawa, tsawon shekaru da dama.
Ko kwanaki biyu kafin zuwan Atiku kamfen a Katsina, wakilin PREMIUM TIMES na Katsina ya tsallake kwanton-ɓaunan ‘yan bindiga da kyar a dajin jihar Katsina, yayin komawa Katsina daga Zamfara.
A kamfen ɗin da Atiku ya je Katsina, ya ce PDP ta bunƙasa jihar Katsina sosai, don haka jama’a su sake fitowa su zaɓi jam’iyyyar domin ta sake share masu hawaye kamar yadda ta yi a baya.
A ziyarar da ya kai Fadar Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir, Atiku ya bayar da gudummawar tallafin kuɗi naira miliyan 50 domin raba wa ‘yan gudun hijirar da ke sansanoni daban-daban a faɗin jihar. Masu gudun hijirar dai ‘yan bindiga su ka fatattake su daga garuruwan su.
Baya ga masifar ‘yan bindiga a Jihar Katsina, jihar na daga sahun jihohin da talauci da ƙuncin fatara ya yi wa talakawan ta katutu, kamar yadda rahoton Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Fatara da Talauci da sauran bayanai, wato ‘National Bureau of Statistics ta bayyana.
A farkon watan Fabrairu ne kuma APC ta roƙi kada ‘yan Najeriya su zaɓi ɗan takarar da ke niyyar buɗe ‘boda’.
Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta Bola Tinubu, ta yi gargaɗi da roƙo ga manoman Najeriya cewa kada su zaɓi ɗan takarar da ke da niyyar idan ya zama shugaban ƙasa zai buɗe kan iyakokin Najeriya.
Daraktan Harkokin Noma na kamfen ɗin Tinubu, Abubakar Bello ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya ke ganawa da kungiyoyin manoma a Hedikwatar APC da ke Abuja.
Bello ya ce kada manoma su yi fargar jajin zaɓen wanda idan ya hau mulki zai maida hannun agogon ayyukan bunƙasa noma da wannan ta yi a baya.
“Kada mu yi sakaci, sagegeduwar tafka kuskuren da zai kai mu ga samun shugaban da idan ya hau sau buɗe kan iyakokin Najeriya ta ƙasa. Saboda mun gani a labarai wani ɗan takarar shugaban ƙasa na cewa idan ya yi nasara zai buɗe kan iyakokin Najeriya. To me wannan abu zai haifar wa ‘yan Najeriya kenan?
“Za shi maida mu shekarun baya, lokacin da shinkafa ma sai an shigo mana da ita daga waje. Haka makamai, kuma matasan mu za su rasa aikin yi kenan. Dukkan masana’antun shinkafa za su mutu kenan fa murus. Don haka mu tashi mu wayar da kan mambobin mu domin a zaɓi Tinubu.”
Tun cikin 2019 Gwamnatin Tarayya ta rufe kan iyakokin Najeriya da nufin daƙile sumogal.
An buɗe wasu kan iyakokin cikin 2021, amma kuma an haramta shigo da shinkafa, kayan kiwon kaji da sauran su.
Sai dai kuma maimakon a samu sauƙin kayan abinci, sai farashin sa ya nunka nunkin-ba-nunkin, har talakawa na kukan cewa har ma gara lokacin da kan iyakokin ke buɗe, abincin ya fi sauƙin farashi a lokacin.auƙin farashi a lokacin.