A binciken da PREMIUM TIMES ta yi daga majiya mai karfin gaske, ta gano cewa an samu karancin takardun buga sabbin kudi ne yasa ake samun karancin su a kasar.
Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele da kansa ya fadi haka a wurin taron kasa da aka yi a fadar gwamanti dake Aso Rock a Abuja.
Taron wanda ya samu halarcin tsoffin shugabannin Najeriya hudu, da suka hada da Yakubu Gowon, Goodluck Jonathan, Abdussalami Abubakar da Olusegun Obasanjo.
Emefiele ya fadi wa tsoffin shugabannin Najeriyan cewa karancin takardun buga kudi ne ya sa ake samun tafiyar hawainiya a sauya tsoffin takardun kudi zuwa sabbi da ake samu a fadin kasar nan.
Emefiele ya ce, Yanzu haka mun aika kasashen Ingila da Jamus domin su buga mana takardun buga naira 500 da 1000. Sai dai kuma sun ce ba za mu samu ba nan kusa za mu bi layi ne muma.
Sauya launin takardun kudid Najeriya ya jawo tashin hankali da matsalolin gaske a fadin kasa Najeriya inda a jihohin Ogun da Ondo ka yi kazamar zanga-zanga domin kushe wa’adin da gwamnati ta saka na daina amfani da tsoffin kudin.
Idan ba a manta ba, gwamnonin Kaduna, Zamfara da Kogi sun kai karar gwamnatin tarayya kotun koli kan wa;adin 10 ga wata da Babban Banki ya saka. Kotun ta yanke hukuncin a dakatar da maganar wa’adin sai an gama sauraren hukuncin da kotun za ta yanke nan gaba.
Ko da yake gwanatin tarayya ta ce kotun koli bata da hurumin yanke irin wannan hukunci, ba ta ce komai ba game da wannan hukunci.
Discussion about this post