Jami’an hukumar EFCC sun yi won gaba da manajan wani banki tare da ma’aikatan bankin da suka boye naira miliyan 29 suka ki sakawa a ATM sannan suka ki biyan jama’a da suka yi cincirindo a wajen bankin suna jira tun safe kuma aka ce musu babu kudin.
Kakakin hukumar Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa jami’an sun kai samame ba zata wannan banki da ke Abuja suka bukaci a bude musu inda aka ajiyar kudi su gani.
Nan take suka bankado naira miliyan 29 da bankin ta boye don yin harkalla da su.
Jami’an hukumar sun tasa keyar manajan bankin sannan suka umarci bankin ta saka kudaden duka a na’urorin ATM din su sanna su rika biyan mutane kai tsaye a cikin bankin.
Babban Bankin Najeriya ya ce ba zai kara wa’adin kwanaki 10 da ya kara ba na wa’adin canja kudi da ajiyar su.
Mutane na ci gaba da bin dogayen laye a bankuna domin samun sabbin kudi don harkokin yau da kullum.
Discussion about this post