Kasar Amurka ta kai karar wasu ma’aikatan jinya dake aikin nas guda 18 ‘yan Najeriya kotu bayan an kama su da jabun takardun kammala karatun nas.
Hukumar kula da aikin Nas dake Texas ce ta shigar da karar a kotun Lardi na Kudancin Florida sannan kotun ta gurfanar da ma’aikatan jinyar bisa laifukan da suka hada da samun takardun boge na kammala karatun aikin jinya da samun lasisin yin aikin na karya.
Wakili na musamman dake kula da binciken kama wadannan ma’aikata Omar Aybar ya ce siyarwa da siyan takardun kammala karatun aikin jinya da lasisin aikin ga mutanen da ba su karancin aikin ba babban laifi ne da zai iya halaka mara lafiya.
Makarantun aikin nas da aka kama sun hada da kwalejin Siena dake gundumar Broward, Fla-school of Nursing a Palm Beach County, Fla- Sacred Heart International Institute dake gundumar Broward County.
Masu bincike na FBI sun ce an rufe wadannan makarantun.
’Yan Najeriyan da aka kai kara sun hada da Abiodun Felicia, Adelakun Aveez, Adelekan Adewale, Adeoye Temitope, Adewale Abidemi, Afolabi Toun, Afolabi Omowunmi, Agbo Steve da Ajibade Omotayo.
Sauran sun hada da Akande Olabisi, Akhigbe Catherine, Akinrolabu Folasade, Ako Esiri, Akpan Rosemary, Alimi Bukola, Ani Ndirika, Aroh Nchekwube da Ayodeji Sherifat.
Laifufuka irin haka na yawan faruwa a Amurka sannan bisa ga dokar kasar hukuncin laifi irin haka shine daure mutum a gidan yari na tsawon shekara 20.
Discussion about this post