Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya yi wani taƙaitaccen jawabi, amma fa mai ratsa jiki sosai, a lokacin da ya ke gabatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Zulum cewa ya yi Tinubu bai yi watsi da Jihar Barno ba a lokacin da jihar ke cikin matsanacin halin da ba ta samu kan ta a tsawon shekaru 1,200 na tarihin Barno ba. Yayin da wasu da dama su ka juya baya daga ziyarar Maiduguri, saboda ganin ta zama wani filin gumurzun Boko Haram, shi kuwa Asiwaju Tinubu ya nuna juriyar kai ziyara can, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba.
Zulum ya ci gaba da yi wa Shehun Borno bayani, “Lokacin da Borno ta shiga mawuyacin hali, Tinubu ya sha kawo ziyara, kamar sau bakwai ko sau takwas a cikin shekaru sha ɗaya. Kuma ina tabbatar maka babu wani da ya yi mana haka, sai dai shi.”
Wannan kyakkyawar shaida da Zulum ya bayar kan Tinubu, ba a shekarun baya-bayan irin wannan zumuncin ya ƙullu tsakanin sa da Arewacin Nijeriya ba. Ba zumunci ba ne na ‘yan a-rama-wa-kura-aniyar-ta ba. Zumunci ne na abokantaka da kyakkyawar zamantakewa. Shi ya sa ba wani abin mamaki ba ne ganin irin gagarimar karɓuwar da Asiwaju ya yi a Arewa.
Babbar alamar gane irin karɓuwar da ya yi a Arewa, ita ce irin cincirindon jama’ar da ke fitar-farin-ɗango zuwa wurin kamfen ɗin sa a jihohin Arewa. Tun daga Kaduna, tsohuwar hedikwatar Arewa zuwa Kano, cibiyar kasuwancin Arewa, har zuwa daulolin mashahuran sarautun gargajiya biyu na Arewa, wato Daular Fulani ta Sokoto da kuma Borno, Daular Kanuri.
Mamaki ya kama wani yayin da ya ga hoton dandazon mutanen da su ka halarci ɗaya daga cikin wuraren kamfen ɗin Asiwaju a Arewa. Sai ya shiga shafin sa na tiwita cike da al’ajabi, ya rubuta cewa: “Yan Arewa fa sun fi kowa ɗaukar batun Tinubu da muhimmanci.” To ai kuwa maganar sa gaskiya ce, saboda ‘yan Arewa sun iya bayar da gaskiya da amanna ga abu mafi cancanta. Na biyu kuma shi ne sun yarda wannan ne lokacin da ya fi dacewa su nuna wa Tinubu godiyar su dangane da daɗaɗɗe kuma kyakkyawan zumuncin da ke tsakanin su.
Dalili kenan duk wani haƙilo da kitimirmirar da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar da ‘yan-koren sa su ka yi ta kitsawa domin ruruta ƙiyayyar ƙabilanci da ɓangaranci, ba su yi nasara a Arewa ba. Saboda mafi yawan mutane ba su ɓata lokacin sauraren su, ko maida hankali a kan su ba.
Tambayar da kawai mutane ke yi a batun masu neman shugabancin ƙasa, ita ce shin ne ɗan takara wane ya taɓa yi wa Arewa da jama’ar ta, har zai cancanci su zaɓe shi? Hakan kuwa ai mutane sun yi gaskiya, domin za su fi so a ce su na tare da wanda a duk lokacin da su ke cikin wani hali, shi ya na tare da su, ba ya gudun su kamar yadda wasu ke yi a Arewa, sai ranar neman biyan buƙatar mutum sannan zai wanke riga ya garzaya Arewa.
Tarihi ko na ce labarin daɗaɗɗiyar alaƙar kusancin Asiwaju da Arewa ya na da tsawo sosai. Sai dai na ɗan yi tariyar baya kaɗan na ɗan taƙaita. Saboda hatta ita kan ta farkon tafiyar Tinubu bisa turbar siyasa, daga Arewa ya fara ta ɗungurugum. A lokacin da aka fara siyasar rusasshiyar Jamhuriya ta Uku, sai Tinubu ya shiga rundunar siyasar marigayi Shehu ‘Yar’Adua, a lokacin da ɗan ƙabilar sa Lateef Jakande shi ma ya fito takara.
A shekarar da marigayi MKO Abiola ya fito takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin SDP, Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wajen ɗaukar Babagana Kingibe a matsayin mataimakin takarar Abiola.
A baya-bayan nan kuma, Tinubu ya ɗauki gaban-gabarar nuna cikakken goyon gaba ga ‘yan Arewa masu takarar shugabancin ƙasa, har sau huɗu ɗaya bayan-ɗaya, a lokuta daban-daban.
Asiwaju ya goyi bayan Atiku a 2007, sai Nuhu Ribadu a 2011, ga Muhammadu Buhari har sau biyu, a 2015 da 2019. Waɗannan kenan, banda ma wasu masu ɗimbin yawa da ya tallafa wa su ka samu matsayi ko nasarar muƙamai, ba don wata biyan buƙata ba. Amma da ya ke ɗan Adam saurin manta baya gare shi, Atiku da Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ai duk sun ci albarkacin Tinubu a 2011. Domin Asiwaju ne ya shiga gaban bataliyar da ta ciwo wa Tambuwal yaƙin da ya kai shi yin nasarar zama Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa a 2011.
Idan mu ka fita daga batun siyasa kuwa, Tinubu a koda yaushe ya na tare da Arewa a duk lokacin da yankin ya shiga mawuyacin hali. Ya na ɗaukar matsalar da muhimmanci, tamkar shi ma ɗan Arewa ne cikakke. Kuma hakan ya ke nunawa a sauran yankunan ƙasar nan baki ɗaya, ta hanyar ɗaukar nauyin magance abin da bai fi ƙarfin iyawar sa ba. Ya je har Zamfara da Birnin Gwari ya jajenta wa waɗanda ‘yan bindiga su ka ƙuntata wa, ya ƙarfafa masu guiwa, kuma ya bayar da tallafi. Banda Asiwaju babu wanda ya je irin waɗannan wuraren sai fa da ƙafar su ta kai su lokacin kamfen.
A kwanan nan da zaɓen shugaban ƙasa ya kusanto, ‘yan adawa na ta gaganiya da kiciniyar shafa wa Tinubu baƙin fenti. Sun ƙirƙiri ƙarairayi sun yaɓa a kan sa. Mutumin da ya kashe kaifin hargagin ‘yan OPC a Legas, kuma ya mutunta Hausawa mazauna Legas, wai shi ‘yan adawa ke zargi da kishiyar abin da ya yi.
Ku tuna lokacin da Tinubu ya je Dakin Taro na Arewa House, Kaduna, ya yi maganganun da su ka ratsa jini da jijiyoyin dattawan Arewa, ciki kuwa har da ‘yan ga-ni-kashe-nin Atiku, to duk wasu ‘yan jagaliyar da a yanzu za su fito su ce wai Tinubu ba shi da wani daftarin bunƙasa Arewa ai sun makara.
‘Yan Arewa mazauna Legas sun fito sun bayyana yadda Tinubu da tsare-tsaren da ya aiwatar ya kai su ga samun damar da su ka samu karsashin rayuwa sosai a Legas. A yanzu haka akwai Bakatsine kwamishina a Jihar Legas, wanda wannan al’adar kuwa Tinubu ne ya fara ta, ya assasa ta. Kuma an zaɓi wasu da dama an ba su matsayi daban-daban. Miliyoyin ƙananan yara ‘yan Arewa sun amfana da tsarin bayar da ilmi kyauta da Tinubu ya ƙirƙira a Legas.
Da farko ‘yan adawa sun fara da yarfen cewa Tinubu ba shi da cikakkar lafiya. Amma sai ya kunyata su ta hanyar zirga-zirgar fita kamfen ɗin da ya ke yi da har yau bai sare ba, bai nuna gajiyawa ko kasala ba.
Saboda haka tunda yanzu ƙaryar ‘yan adawa ta ƙare, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su zaɓi ɗan takarar da za su iya damƙa wa amanar kan su da ƙasar su, wanda ya ke da tarihin aiwatar da gagarimin ayyukan ci gaba, wanda ya taɓa shafe tsawon lokaci ana cin moriyar ayyukan ci gaban da ya samar a zahiri.
Asiwaju na da kyawawan alamomin samun nasara a zaɓen da za a gwabza ranar Asabar. Saboda ya na da ɗimbin magoya baya, waɗanda ba su bayar da kai borin masu yaɗa siyasar ƙabilanci ya hau kan su ba.
Arewa dai ba ta manta da irin zumunci, abota da kyakkyawar alaƙar ta da Tinubu ba. Mutanen yankin sun tabbatar da cewa su ba al’ummar da ke rama alheri da sharri ba ne. Dalili kenan ma su ka shirya tsaf, zaman jiran zuwan ranar zaɓen shugaban ƙasa, domin su rama wa Tinubu alheri da alheri.
Abdulaziz shi ne Mataimaki Na Musamman A Fannin Yaɗa Labarai, na Asiwaju Tinubu.
Discussion about this post