‘Yar taratsi kuma tsohuwar mamba ɗin da ta fice daga Kwamitin Kamfen ɗin Bola Tinubu a APC, Naja’atu Mohammed, ta yi zargin cewa Uwargidan Shugaban Ƙasa A’isha Buhari ma ta na cikin masu-hana-ruwa-gudu a Fadar Shugaban Ƙasa, wato ‘cabals’.
Naja’atu ta yi wannan zargin a ranar Litinin cikin wata tattaunawa da aka yi a ita a gidan talabijin na Arise TV.
Naja’atu ta yi wannan bayani ne biyo-bayan iƙirarin da Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi.
El-Rufai ya yi zargin cewa akwai wasu manyan jangwalagwadan ƙadangaru a cikin Fadar Shugaban Ƙasa, waɗanda ba su fatan APC ta yi nasara a zaɓen 2023.
Ya ce aiki su ke yi a ɓoye wurjanjan, domin kada Bola Tinubu ya yi nasara a zaɓen na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Yayin da El-Rufai bai ambaci sunayen kowa ba, ita kuwa Naja’atu ta ce A’isha Buhari na cikin manyan ƙadangarun Fadar Shugaban Ƙasa, waɗanda ba su so Tinubu ya yi nasara.
“Masu-hana-ruwa-gudu ai wani gungun manyan jangwalagwadan ƙadangaru ne da ke kewaye da mai mulki, masu riƙe da tsarin da ake tafiyar da gwamnati. Sai abin da su ke so gwamnati za ta yi. A ɓoye su ke aika-aikar su. To ku sani, A’isha Buhari na cikin su.
“A’isha na cikin su, irin su marigayi Abba Kyari, su Mamman Daura.”
Naja’atu ta ce don A’isha Buhari ta tura jawabin El-Rufai a shafin ta na Tiwita, hakan ba zai iya fitar da ita daga gungun manyan jangwalagwadan ƙadangarun da ke hana ruwa gudu a Fadar Shugaban Ƙasa ba.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Aliyu Abdullahi, Kakakin Yaɗa Labaran A’isha Buhari, wanda ya yi alƙawarin zai nemi iznin ogar sa tukunna kafin ya yi magana. Amma dai har aka buga labarin nan bai kira an ji ta bakin sa ba.
Amma wata nahiyar kusa da uwargidan Buhari, ta ce zai yi wuya A’isha ta fito ta na ce-ce-ku-ce da Naja’atu Mohammed.
“Naja’atu suna ko jama’a ta ke so su raja’a kan ta. Taratsin neman cika aljihun ta kawai ta ke yi, ba wani abu ba.” Cewar majiyar.
Discussion about this post