Abdul Ningi na jami’yyar PDP ya lashe zaben kujerar sanatan Bauchi ta Tsakiya a karo ta biyu.
Ningi ya rike mukamin mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa daga 2011 zuwa 2015.
Baturen zabe Ibrahim Danjima ya sanar da sakamakon zaben ranar Litini a wurin tattara sakamakon zabe na jihar dake garin Darazo a karamar hukumar Darazo.
A zaben, Ningi ya samu kuri’u 204,878 sannan abokin hamayyar sa Uba Ahmad-Nanan na APC da ya samu kuri’u 84,621.
Isah Hamman Misau na jami’yyar NNPP ya samu kuri’u 17,995
Discussion about this post