Gwamnatin Tarayya ta umarci a rufe dukkan jami’o’in ƙasar can domin ɗalibai su samu damar yin zaɓen 2023.
Za a kulle jami’o’in ne daga ranar 22 ga Fabrairu zuwa 14 ga Maris, kafin da kuma bayan zaɓe.
Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da jama’a da ƙungiyoyi daban-daban su ka riƙa yi, domin idan su ka kasance a kulle, to an tauye wa ɗaliban damar yin zaɓe kenan.
Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ne ya bai wa Hukumar Kula da Jami’o’i wannan umarni.
Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Chris Maiyaƙi ne ya sa wa sanarwar hannu.
Idan ba a manta ba, a makon ƙarshen watan Janairu Majalisar Tarayya ta umarci Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantu, don ɗalibai su je su yi zaɓe.
Majalisar Tarayya ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta rufe dukkan jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare, domin ɗalibai su samu damar tafiya gida su yi zaɓen 2023.
Majalisar ta umarci Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), NBTE, NCCE da Ma’aikatar Ilmi su rufe dukkan manyan makarantun ƙasar nan domin ɗalibai su je su jefa ƙuri’a.
Sannan kuma majalisa ta umarci INEC ta samar da wani tsari na musamman, wanda zai bai wa ɗalibai damar karɓar katin shaidar rajistar zaɓen su a sauƙaƙe.
Ɗan Majalisar Tarayya Ibrahim Tukura, wanda ɗan APC ne daga Jihar Kebbi, shi ya fito da wannan buƙata, kuma aka amince da ita nan take a ranar Alhamis.
Za a gudanar da zaɓe shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da dattawa a ranar 25 Ga Fabrairu, 2023, sai kuma na gwamnoni da na ‘yan majalisar tarayya a ranar 11 Ga Fabrairu, 2023.
Honorabul Tukura ya ce akwai buƙatar bai wa ɗalibai damar tafiya su yi zaɓe, “saboda a sunayen waɗanda su ka sabunta rajista, akwai ɗalibai har miliyan 3.8.
“Adadin yawan ɗaliban da su ka sabunta rajista ya kai kashi 40.8 kenan na yawan masu rajistar.”
Ya ce, “waɗannan ɗalibai har miliyan 3.8 duk yi rajista ne a garuruwan su, ba a garuruwan da su ke karatu ba. Saboda haka akwai wajibcin a ba su damar zuwa gidajen su ko garuruwan su domin su yi zaɓe.”
Ya ce kuma ya kamata a ba ɗalibai damar karɓar PVC ɗin su a sauƙaƙe.
“Yayin da INEC ke ci gaba da aikin raba katin zaɓe a yanzu, su kuma ɗalibai hankulan su ya rabu su na can su na darussa a makarantun su. INEC kuma na aikin raba kati a faɗin ƙananan hukumomi 774. Hakan ya tauye masu lokacin fita su karɓi katin su.”
Daga nan take aka umarci Kwamitin Kula da Manyan Makarantu ya haɗa kai da hukumomin ilmi da INEC domin a samu nasarar bai wa ɗalibai damar fita su yi zaɓe.