Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu ɓarayin mutane su biyu sannan kuma sun ceto yara biyu da aka yi garkuwa da su a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mamman Dauda ya ce jami’an tsaron sun kama Nura Auwal Mai shekara 22 mazaunin kwatas din Rijiyar Lemo da abokin sa Abubakar Lawal shima mai shekaru 22 dake zama a Kwatas din Bachirawa tare da wasu yara biyu a Wani kangon gini inda suka boye su.
Dauda ya ce rundunar ta kama wadannan mutane ne biyu bayan Wani Isyaku Salisu da Auwal Sale mazaunan kwatas din Bachirawa dake karamar hukumar Ungogo sun kawo kara ofishin ƴan sanda cewa an ayi garkuwa da ‘ya’yan su daya Umar Isyaku mai shekaru 3 da Aliyu Auwal mai shekaru 4.
Ya ce Iyayen wadannan yara sun ce sun samu wasika dake dauke da lambar wayar da lambar asusun banki da za su je su saka kuɗin fansar yaran.
“A wasikar wadanda suka Yi garkuwa da yaran sun ce a biya su Naira miliyan 20 inda daga baya suka amince a biya Naira miliyan 2 akan kowani yaro.
“Nan da nan na aika da rundunar Operation Restore Peace domin ceto yaran da kama wadanda suka yi garkuwa da su.
Dauda ya ce da suka shiga hannun jami’an tsaro Auwal da Lawal sun tabbatar cewa sune suka Yi garkuwa da yaran sannan suka aika da wasika ga Iyayen yaran.
Discussion about this post