Jam’iyyar APC ta umarci Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da Ministan Shari’a Abubakar Malami cewa su gaggauta bin umarnin da Kotun Ƙoli ta bayar dangane da batun tsoffin kuɗaɗe da sabbin kuɗaɗe.
APC ta yi wannan kira a ranar Lahadi, bayan taron da Shugaban Jam’iyya Abdullahi Adamu da Kwamitin Zartaswar APC da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu su ka yi tare da gwamnonin APC, a Abuja.
Gwamnonin da su ka halarci taron sun haɗa da Simon Lalong na Filato, Abdullahi Sule na Nasarawa, Abubakar Bello na Neja, Nasir El-Rufai na Kaduna, Yahaya Bello na Kogi.
Sauran sun haɗa da Inuwa Yahaya na Gombe, Mala Buni na Yobe, Bello Matawalle na Zamfara, Biodun Oyebanji, Ekiti, Babajide Sanwo-Olu na Lagos, Atiku Bagudu na Kebbi da kuma Abubakar Badaru na Jigawa.
Ɗan takarar shugabancin ƙasa na APC, Bola Tinubu ya shiga zauren taron bayan an rigaya an yi nisa daga baya.
Adamu ya karanta wa manema labarai abin da su ka zartas a wurin taron taron cewa Minista Malami da Gwamnan CBN Emefiele tilas su fito su bi umarnin Kotun Ƙoli.
Haka kuma Adamu ya roƙi Shugaba Buhari ya shiga cikin wannan harankazamar domin ya ɗora komai a kan saitin.
Shi ma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu na Kebbi, ya ce gwamnonin jam’iyyyar da shugabannin APC duk kan su a haɗe ya ke.
A cikin makon jiya ma sai da Kakakin Majalisar Tarayya, Gbajabiamila ya caccaki jawabin da Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya.
Kakakin Majalisar Tarayya Femi Gbajabiamila ya bayyana jawabin matsayin da gwamnatin tarayya ta ɗauka, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi yau Alhamis da safe cewa rashin bin umarnin Kotun Ƙoli ne ƙarara.
Gbajabiamila ya yi wa Buhari wannan raddin a cikin wata sanarwar da ya fitar wadda Kakakin Yaɗa Labaran sa, Lanre Lasisi ya sa wa hannu.
A jawabin Buhari dai ya bada umarnin a ci gaba da karɓartsoffin naira 200 har zuwa 10 ga Afrilu, amma an rufe amfani da Naira 500 da kuma 1000.
Gbajabiamila ya ce dawo da amfani da Naira 200 abu ne mai kyau, to amma kuma an kauce wa bin tsarin da hukuncin Kotun Ƙoli ya gindaya.
Ya yi wa Gwamnan Babban Bankin Najeriya wankin babban bargo, inda ya ce ya kasa ceto naira daga faɗuwar darajar ta amma ya fito da tsarin da kowa ke ji a jikin sa a halin yanzu.
A jawabin sa, Buhari ya ce, ya na tausaya wa ‘yan Najeriya, amma tsarin akwai alfanu a cikin sa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na matuƙar tausayin yadda ‘yan Najeriya su ka shiga mawuyacin hali, sanadiyyar ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
A cikin jawabin da ya yi wa ‘yan Najeriya a ranar Alhamis, Buhari ya ce an shigo da wannan sabon tsarin domin a ƙarfafa tattalin arziki, yaƙi da cin hanci da rashawa, inganta hanyoyin daƙile ta’addanci da matsalolin tsaro waɗanda su ka kawo wa Najeriya cikas a harkokin cikin gida da waje.
Ya ce za’a gaggauta bijiro da hanyoyin da ‘yan Najeriya za su samu sauƙin mu’amalar kuɗaɗe da hada-hadar kasuwanci, a gefe ɗaya kuma za’a ci gaba da tsarin bunƙasa tattalin arziki, tare da toshe ƙofofin da ake karkatar da maƙudan kuɗaɗen ƙasar nan.
Buhari ya ce duk da tsananin da ake fuskanta, gwamnati ta fara samun nasarorin dalilin sauya launin kuɗi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nassrorin dalilin sauya launin kuɗi sun fara bayyana, duk kuwa da ƙorafe-ƙorafen halin ƙuncin da jama’a su ka shiga na ƙarancin sabbin kuɗaɗe.
Buhari ya yi wannan bayani a cikin jawabin sa na ranar Alhamis, wanda ya yi wa ‘yan Najeriya, inda ya bayyana damuwa dangane da halin da aka shiga, a gefe ɗaya kuma ya ke jinjina wa nasarorin da ya ce sauya launin kuɗin sun fara samarwa.
Buhari ya yi wannan bayani daidai lokacin da tuni wasu hasalallun matasa sun fara fusata a garuruwa daban-daban, su na banka wa bankunan kasuwanci wuta.
“An shaida min cewa daga lokacin da aka shigo da sabbin kuɗi zuwa yau, naira tiriliyan 2.1 da ake damfare a hannun mutane an mayar da su banki. Wannan kuma babbar nasara ce.”
Buhari ya ce ba zai yiwu a rage tsadar rayuwa ba har sai an rage kuɗaɗen da ke shige-da-fice a hannun jama’a tukunna.
Sannan kuma ya ce sabon tsarin ya daƙile yawancin ayyukan ɓarnar da ake yi ta hanyar tara maƙudan kuɗaɗe ta hanyar da doka ta yi hani a kai.
Domin a samar wa jama’a sauƙin hada-hada, Buhari ya umarci CBN ta halasta karɓar tsoffin naira 200 har tsawon watanni biyu, wato zuwa 10 Ga Afrilu.