Ɗan takarar Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdul’aziz Yar’Adua na APC ne ya yi nasarar lashe zaɓen a jihar Katsina, inda ya samu ƙuri’u 153,512. Na PDP Aminu Sirajo kuwa ya samu 152,140.
Abdul’aziz tsohon Laftanar Kanar ne mai ritaya. Shi ne ya maye gurbin Sanata Kabir Barkiya, wanda ya sha kaye tun a zaɓen fidda gwani.
Wani sakamako daga jihar Gombe kuma ya nuna Atiku ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Gombe, ya nunka Tinubu samun ƙuri’un jihar.
Ɗan takarar shugabancin ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ya lashe dukkan ƙananan hukumomin Jihar Gombe 11.
Baturiyar Zaɓe Farfesa Maimuma Waziri ta bayyana Atiku ya samu ƙuri’u 319,123, shi kuma Bola Tinubu na APC ya samu 146,977.
A Ƙaramar Hukumar Gombe ce Atiku ya fi samun yawan ƙuri’u har 62,347, sai Akko 55,202, sai kuma Yamaltu Deba 38,479.