Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce wasu jami’an gwamnatin tarayya sun kira shi a waya, kuma sun kira wasu gwamnonin, su na so a sasanta shari’ar da mu ke gwabzawa a wajen kotu.
Sai dai El-Rufai ya ce ya ƙi karɓar tayin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi masu, inda ta ce ta bada zaɓin a ci gaba da karɓar tsoffin naira 200 har zuwa 10 Ga Afrilu, amma gwamnonin da su ka kai ƙara su janye.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na El-Rufai, wato Muyiwa Adekeye ya fitar a ranar Laraba, ya ce rahoton da wata jarida ta buga cewa wai Gwamnonin Najeriya sun gana har kusan asubahin ranar Laraba su da gwamnatin tarayya, ba gaskiya ba ne.
Ya ce ba a yi wata ganawa tsakanin su ba. Maimakon haka, wasu jami’an gwamnatin tarayya sun kira shi, su ka miƙa tayin cewa za a bar tsoffin naira 200 a ci gaba da karɓar su har nan da wata biyu, amma gwamnonin da su ka kai ƙara su janye.
Ya ce gwamnatin tarayya ta yi iƙirarin wai tuni ta lalata kuma ta ƙone dukkan tsoffin kuɗaɗe na naira 500 da Naira 1000 waɗanda ta rigaya ta karɓe daga hannun jama’a. Sun ce CBN ne ya ƙone kuɗaɗen.
El-Rufai ya ce shi bai yarda CBN ya ƙone ko ya lalata dukkan tsoffin naira 500 da 1000 ɗin da aka karɓa daga hannun mutane ba.
El-Rufai ya ce sun ƙi amincewa saboda a dawo ana amfani da tsoffin naira 200 ba zai magance gagarimar matsalar ƙuncin rayuwar da ‘yan Najeriya su ka shiga a sakamakon canjin kuɗaɗe ba.
Idan ba a manta ba, gwamnoni sun fusata kwanan baya sun bayyana cewa:
‘Ƙwace Emefiele Ya Yi Wa ‘Yan Najeriya, Ba Canjin Kuɗi Ba:
Gwamnonin Najeriya sun ce Babban Bankin Najeriya ba wata basira ba ce da ya ƙirƙiro sauya launin kuɗi, sai kawai ƙwace ne ƙiriƙiri bankin ya yi wa kuɗaɗen jama’a, ya tara ya kimshe a hannun sa.
Gwamnonin Najeriya sun ce CBN ya gaggauta janye wa’adin da zai daina amsar tsoffin kuɗi, a ƙyale kowa ya ji da abin da ya ishe shi.
Sun bayyana haka a taron ganawa da su ka yi a Abuja ranar Asabar.
‘Ƙwacen kuɗi Emefiele ya yi wa jama’a ba canjin kuɗi ba’ -Gwamnonin Najeriya:
Cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, gwamnonin sun ce “CBN abin da CBN ke ci gaba da yi, ba canjin kuɗi ba ne, ƙwacen kuɗaɗe ne kawai da rana tsaka su ke yi wa jama’a. Amma wannan tsiya da ba ta yi daidai dokar musayar kuɗaɗe ta Sashe na 20(3) na Doka wadda CBN ya ginu a kai, ta shekarar 2007.
“Ƙwacen kuɗaɗe ne mana domin an ƙwace kuɗaɗen jama’a, su kuma waɗanda ke sabbi babu su kwata-kwata babu alamar su. Waɗanda aka ce an buga ba su wadata ba.
Wannan kakkausan bayani na ƙunshe ne a cikin takardar bayan taron da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya sa wa hannu.
Gwamnonin sun cimma wannan matsayar ce ganin irin halin ƙuncin da aka jefa ‘yan Najeriya ba rashin kuɗi, musamman ma
talakawa.
Gwamnonin na Najeriya sun gargaɗi CBN cewa wannan bahangurɓar canjin kuɗi za ta haifar da karayar tattalin arzikin Najeriya.
Sun ce fito da wannan tsarin taƙaita hada-hada da takardun kuɗaɗe ba abu ne da zai yi tasiri yanzu-yanzu a ƙasar nan kamar ɗibar wuta ba.
Sun ce idan ba a yi da gaske an shawo kan lamarin ba, to CBN zai kawo mummunan ruɗani ga tattalin arzikin Najeriya, wanda idan ya karye, to ɗora shi sai fa maɗoran asali.
A ranar Laraba ce kuma Kotun Ƙoli ta ɗaga shari’a, ta bar ‘yan Najeriya a duhu.
Kotun Ƙoli ta ɗage sauraren ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar, inda ta ƙalubalanci gwamnonin APC uku waɗanda su ka nemi a ƙara wa’adin karɓar tsoffin kuɗaɗe daga hannun ‘yan Najeriya.
A ranar 8 Ga Fabrairu aka shigar da ƙarar, inda Kotun Ƙoli ta ce za a zauna ranar Laraba, 15 Ga Fabrairu.
A zaman na ranar Laraba, alƙalai bakwai na Kotun Koli ne su ka zauna sauraren shari’ar, wadda dukkan gwamnonin uku da su ka kai ƙarar sun halarta.
Sai dai kuma an ɗage sauraren zuwa ranar 22 ga Fabrairu, amma kuma kotun ba ta ce a ci gaba da karɓa ko kada a ci gaba da karɓa ɗin ba.
Mutane sun shiga ruɗu, domin kafin zaman kotun na ranar Laraba, an yi tsammanin jiran ko ita Kotun Ƙoli ɗin za ta yanke hukuncin daina karɓa kwata-kwata, ko kuma ci gaba da karɓa kawai.
Jama’a na ƙara shiga ruɗu ganin yadda a wasu jihohin mutane ke kwana kan layin cirar kuɗi a ATM, ga kuma an daina karɓar tsoffin kuɗaɗe, waɗanda tuni CBN ya fitar da tsarin yadda mai tsoffin kuɗi zai maida su CBN ɗin.
Wannan jarida ta ruwaito Emefiele a ranar Talata ya ce, “ba ruwa na da umarnin Kotun Ƙoli, duk mai tsoffin kuɗi a hannu ƙaranga ya ke riƙe ba naira ba”.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu ruwan sa da umarni ko hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke a makon da ya gabata, ko wanda za ta yanke a ranar 15 Ga Fabrairu.
Ya ce duk wani mai riƙe da tsoffin kuɗin Naira 200, 500 da kuma 1000, to ba shi da bambanci da mai kayan ƙarangar takardar tsire, domin ba zai iya hada-hada da kuɗin a yanzu ba.
Ya faɗi haka ne a ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara Ma’aikatar Harkokin Waje, a Abuja.
A ranar 8 Ga Fabrairu Kotun Ƙoli ta ƙara kwana bakwai daga wa’adin 10 Ga Fabrairu wanda Emefiele ya ƙara lokacin da ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Daura.
Sai dai kuma tun bayan da Kotun Ƙoli ta yi ƙarin wa’adin, CBN ba ta yi magana ba, sai yau, jajibirin ranar ƙarewar wa’adin, kafin a ji abin da Kotun Ƙoli za ta zartas kuma ranar Laraba, 15 Ga Fabrairu.
A ranar Litinin dai mafi yawan masu manya da ƙananan kasuwanci sun daina karɓar tsoffin kuɗaɗe. Amma lamarin ya fi muni a ranar Talata.
A ranar Talata ɗin ce kuma Emefiele ya bayyana cewa CBN ba zai ƙara ko kwana ɗaya daga tsohon wa’adin da ya bayar ba.
“To ai yanzu lamarin ya yi sauƙi sosai, tunda bankuna sun fara biyan mutane kuɗaɗe a kan kanta. Kuma masu POS su ma su na biyan kuɗaɗen.” Inji Emefiele.
“Saboda haka babu buƙatar a ƙara ko da wa’adin rana ɗaya kuma daga 10 ga Fabrairu.”
Emefiele ya zargi wasu ‘yan siyasa da laifin ɓoye sabbin kuɗaɗe.
“Wasu shugabannin mu su na sayen sabbin kuɗaɗe su na ɓoyewa, su na kimshewa saboda wasu dalilai. Ba na son bayyana abin da za su yi da kuɗin.” Inji Emefiele.
Discussion about this post