Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ƙirƙiro tsarin sauya launin kuɗi ne kawai da gangan, a matsayin ramuwar-gayyar kasa samun tikitin takarar shugaban ƙasa da ya yi a ƙarƙashin APC.
Haka Ganduje ya bayyana a wurin gangamin kamfen ɗin APC a garin Tsanyawa, a ranar Lahadi.
“Kawai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefiele ya ƙirƙiro canjin launin kuɗi ne don ya rikita ‘yan Najeriya. Babu wani dalili banda wannan.
“Emefiele ya daɗe ba ya cikin yanayi na nishaɗi da farin ciki, saboda haushin bai samu tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ba a wannan babbar jam’iyyar ta mu, APC.” Inji Ganduje.
Ganduje ya ce Gwamantin Jihar Kano da APC Reshen Jihar Kano duk ba su goyon bayan ƙirƙiro sauya launin kuɗi a daidai wannan lokaci.
“A faɗin duniyar nan ƙasashe da dama su na canja kuɗaɗen su, amma su ba irin tsarin shirme su ke bi ba, irin wannan shirmen da Emefiele ya yi. Lokacin canja kuɗin bai yi daidai ba, haka nan wa’adin da aka bayar na daina amfani da tsoffin kuɗaɗe nan da 10 Ga Fabrairu, shi ma ya yi kaɗan, kuma duk da gangan Emefiele ya yi haka, ya na sane.
Ganduje ya ce zai kira manajojin bankunan da ke Jihar Kano domin a samu mafita daga matsalar ƙarancin kuɗaɗe da al’ummar jihar sa ke ciki.
Shi ma tsohon Shugaban APC, Adams Oshiomhole, ya ce Emefiele ya ƙirƙiro canjin launin kuɗi don ya haddasa fitinar da za ta hana yin zaɓen 2023.
Tsohon Gwamnan Jihar Edo, kuma tsohon Shugaban APC, Adams Oshiomhole, ya ce idan ba a magance matsalar sauya launin kuɗi ba, to hargitsi na iya ɓarkewar da zai yi munin da tilas sai an ɗage zaɓe 2023.
Oshiomhole wanda shi ne Mataimakin Babban Daraktan Kamfen na Bola Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, ya bayyana tsarin sauya launin kuɗin da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ƙirƙiro a daidai wannan lokaci cewa rashin tunani ne.
Oshiomhole ya ce, idan ma CBN na nufin ya ƙirƙiro canjin kuɗi ne don hana sayen ƙuri’u, “to ai ba aikin CBN ba ne hana sayen ƙuri’u ɗin.”
A ranar Lahadi Oshiomhole ya yi wannan bayani a lokacin da ake tattaunawa da shi a gidan talabijin na Channels TV.
“Idan aka samu tarzoma kamar yadda ta faru a Benin da Ibadan, ban sani ba ko an yi a waɗansu wuraren. Kuma aka ci gaba da tarzomar a garuruwa daban-daban, shin gwamnati za ta koma ta kan zaɓe, tunda ta maida hankali kan kwantar da hargitsi domin samun zaman lafiya?
“Don haka kawai ni dai abin da zan ce shi ne wanda ya ƙirƙiro canjin launin kuɗi ya yi ne don ya hana APC yin nasara a zaɓen 2023.
“Idan ka duba da kyau, za ka gane cewa nufin CBN kawai shi ne ya hana a gudanar da zaɓen 2023, ba wai hana wulaƙantar da naira ba.” Haka Oshiomhole ya yi iƙirari.
Baya ga Bola Tinubu, sauran jiga-jigan APC da su ka la’anci sauya launin kuɗi sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yami Osinbajo, Gwamna Nasir El-Rufai da Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano.
Sai dai kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar da Peter Obi na PDP duk sun goyi bayan canjin kuɗin.