Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Bankin Duniya (World Bank), kuma tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Oby Ezekwesili, ta bayyana cewa an ƙirƙiro sauya launin kuɗi ne don a magance maɓarnatan ‘yan siyasa masu amfani da muggan kuɗaɗe don su biya buƙatar su.
To sai dai kuma ta ce akwai hanyoyin da ya kamata a ce an bi an taka masu burki, ba sai an ƙaƙaba canjin kuɗin da a yanzu haka ya jefa talakawa cikin matsanancin halin ƙuncin rayuwa ba.
Da ake tattaunawa da ita a gidan talabijin na Channels TV, Obey ta ce, “waɗannan muggan ‘yan siyasa kuma ɓarayin gwamnati ai duk gwamnatin ta san su, domin a cikin ta su ke, tare da juna su ke. To me zai hana a dira ta kan su kawai, ba sai an ƙirƙiro tsarin da zai gallaza wa miliyoyin waɗanda ba su da laifin tabka ɓarnar ba?”
“A matsayi na na wacce ta san harkokin kuɗaɗe, ina tababa idan akwai ƙwararrun masana harkokin tattalin arziki a cikin CBN. Domin idan akwai waɗanda su ka san abin da su ke yi, ba za su bayar da shawarar a yi tsarin canjin kuɗin nan ba.”
Oby wadda ke goyon bayan takarar Peter Obi na LP, ta ce babu hujjar da zai sa ta zaɓi Atiku Abubakar na PDP ko Bola Tinubu na APC, saboda a cewar sa, su biyun duk ba su cancanta ba.