Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa motar da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ba shi mai sulke, ita ce silar tsira da ran sa, a lokacin da aka kai masa mumnunan harin bam a Kaduna.
Buhari ya bayyana haka a cikin wani faifan bayanin sa da aka watsa a ranar Lahadi, wanda ya yi bayanin irin zaman sa shugaban ƙasa da sauran bayanai kan rayuwar sa da mulkin sa.
An kai masa harin ne a ranar 24 Ga Yuli, 2014, lokacin da ake tsakiyar kamfen ɗin 2014, kafin zaɓen 2015.
An kai masa harin ne daidai Kawo, Kaduna, kan hanyar sa ta zuwa Kano. A harin an kashe mutane da yawan da aka ƙiyasta sun kai 80, waɗanda dukkan su fararen hula ne da ke gefen titi.
Buhari ya ce Kwankwaso ne wanda ya taɓa yin Ministan Tsaro, ya shawarce shi cewa zai ba shi kyautar mota mai sulke, domin tsaron lafiyar sa.
“Ba don Kwankwaso ba da ya ba ni kyautar mota mai sulke, da tuni bam ya kashe ni.
“Kwankwaso ne wata rana ya ba ni shawara cewa waɗanda ke neman mulki ido rufe a 2015 za su iya ƙoƙarin halaka ni. Don haka ya ba ni mota mai sulke saboda kare lafiya da rayuwa ta.
“A ranar da aka nemi kashe ni, mun kai daidai Kawo, a cikin Kaduna, sai wata mota ƙirar Jeep ta nemi wuce mu, amma jami’an tsaro na su ka hana ta wucewa.
“Kawai sai dai tashin bam mu ka ji na cikin motar sun tayar.
“Mu dai a cikin motar mu babu abin da ya same mu. Amma da na dubi jiki na, sai na ga duk jini ne daga jikin waɗanda ke waje da bam ɗin ya ritsa da su.” Inji Buhari.
Buhari ya jinjina wa Kwamkwaso, kuma ya ce mutumin kirki ne, nagari. Kwankwaso ya na cikin masu takarar shugaban ƙasa a halin yanzu. Ya na takara ne a ƙarƙashin jam’iyyyar NNPP.
Discussion about this post